EFCC ta gayyaci tsohon gwamnan Kwara Abdulfatah Ahmed domin ya amsa tambayoyi

EFCC ta gayyaci tsohon gwamnan Kwara Abdulfatah Ahmed domin ya amsa tambayoyi

- Hukumar EFCC ta gayyaci tsohon gwamnan jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed zuwa ofishinta

- Fatah ya tabbatar da wannan gayyata, inda yace ya amsa ta a ranar Litinin, 7 ga watan Disamba harma ya koma gida

- Sai dai yace babu wata tuhuma da ake masa da zamba illa kawai ya fayyace wasu hukunce-hukunce da aka zartar a lokacin da yake jagorantar jihar

Hukumar yaki da cin hanci da hana yi wa tattalin arziki zagon kasa (EFCC) a ranar Litinin, 7 ga watan Disamba ta gayyaci tsohon gwamnan jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed zuwa ofishinta don amsa tambayoyi.

Mista Ahmed ya kasance gwamnan jihar tsakanin 2011 da 2019.

Mista Ahmed, a cikin wata sanarwa da ya saki a shafinsa na Twitter a ranar Talata, ya ce an gayyace shi ne domin fayyace wasu kashe-kashen kudade da kuma zartar da hukunci da aka yi a lokacin da yake rike da jihar.

EFCC ta gayyaci tsohon gwamnan Kwara Abdulfatah Ahmed domin ya amsa tambayoyi
EFCC ta gayyaci tsohon gwamnan Kwara Abdulfatah Ahmed domin ya amsa tambayoyi Hoto: @AbdulfataAhmed
Source: Twitter

KU KARANTA KUMA: A cikin sa'o'i 6, budurwa ta tashi daga Legas zuwa Benin kuma ta koma Legas a babur

Ya wallafa a shafin nasa:

“A jiya, na ziyarci ofishin EFCC na Ilorin bisa gayyata. A yayin zaman, na fayyace wasu kashe-kashen kudi da aka yi da kuma wasu shawarwari da aka zartar a gwamnati a lokacin da nake gwamna. Babu kowani zargi na zamba da aka yi a kaina. Tuni na koma gida.”

Abdulrahman Abdulrazaq wanda ya gaji mulki daga Ahmed ya kafa wani kwamiti don binciken wasu kayayyaki da kadarorin jihar da aka siyar tun daga 1999.

Ya kuma nada wani kwamiti domin duba ga kudaden kananan hukumomi da ayyukansu tun daga 1999, Premium Times ta ruwaito.

Wadannan kwamitoci sun dasa ayar tambaya a kan wasu jami’ai a gwamnatocin baya.

Hakazalika, an gurfanar da tsohon kwamishinan kudi a karkashin Mista Ahmed, Ademola Banu, kan zargin satar kudi naira miliyan 411.

Har ila yau, an gurfanar da tsohuwar shugabar hukumar tallafi na jihar Kwara, Fatimah Yusuf da wasu mutum biyu kan zargin zambar kudade, a gaban Justis Sikiru Oyinloye na babbar kotun jihar da ke Ilorin.

KU KARANTA KUMA: Za a daure bawan Allah da ya bindige zakara

A cewar EFCC an gurfanar da su ne kan tuhume-tuhume bakwai na zarginsu da hannu a zambar kudi naira miliyan 50.

Sai dai kuma ba a hukunta ko mutum guda daga cikinsu ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel