Ta'addanci: Zulum ya karba bakuncin wakilan dakarun sojin Kamaru

Ta'addanci: Zulum ya karba bakuncin wakilan dakarun sojin Kamaru

- Gwamnan jihar Borno, ya tarbi sojojin Kamaru a ranar Alhamis

- Ya bukaci taimakonsu don kawo karshen ta'addanci a jihar

- Yana so su hada karfi da karfe da sojin Najeriya don taimakon yankinsa

Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya tarba sojoji daga Kamaru a ranar Alhamis. Sojojin sun isa gidan gwamnati da ke Maiduguri, babban birnin jihar.

A taron, gwamnan ya bukaci sojojin Kamaru da su taimaka wurin kawo karshen 'yan ta'addan Boko Haram, jaridar Punch ta wallafa.

Kwamandan rundunar soji na 4, Janar Saly Mohammadou, ya jagoranci sojojin Kamaru zuwa gidan gwamnatin.

Kwamandan Sector 1 Multinational joint Task Force, Janar Bouba Debekreo, Birgediya janar Essoh Jules-Cesar, GOC 7 Div Bridgdier, Janar AK. Ibrahim da sauransu ne suka raka su.

Ta'addanci: Zulum ya karba bakuncin wakilan dakarun sojin Kamaru
Ta'addanci: Zulum ya karba bakuncin wakilan dakarun sojin Kamaru. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

KU KARANTA: Ban taba karbar albashi ba tun bayan hawa na kujerar gwamna, Gwamnan APGA

A cewar Zulum, sojojin Kamaru sun zo Najeriya ne don su taya sojojin Najeriya wurin yaki da ta'addanci a wuraren tafkin Chadi.

Kamar yadda yace, "Mafi yawan mutanen Kamaru da Najeriya suna da al'adu iri daya. Duk da rashin tsaron ya shafin yankin tafkin Chadi, kuma hakan ya shafin tattalin arzikinmu. Shiyasa yakamata mu taru mu yaki rashin tsaro.

"Batun siye da siyarwa tsakanin iyaka, dukanmu mun san Banki. Muna iyakar kokarin ganin mun kara bude kasuwar Banki da kuma titunan Banki. Yanzu ya kamata mu bayar da hadin kai wurin kawo karshen rashin tsaro, don jama'a su samu damar yin tafiye-tafiye yadda suka saba."

KU KARANTA: Obasanjo: Dalilin da yasa na hana Gani Adams kawo min ziyara

A wani labari na daban, babban malamin addinin musulunci na jihar Kaduna, Dr Ahmad Abubakar Gumi, ya ce rikicin kudancin Kaduna ya dauki lokaci mai tsawo, Daily Trust ta wallafa.

A cewarsa, ya zama tilas mutanen kirki, maza da mata, su hada karfi da karfe wurin kawo karshen rikicin addinin.

Dr Gumi, wanda shine shugaban KHF ya fara shirin kawo karshen rikicin addini da ke addabar kudancin Kaduna, wanda yake hana cigaba da zaman lafiya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel