NEGF: Kungiyar Gwamnonin Arewa maso Gabas ta yi taro a Jihar Adamawa

NEGF: Kungiyar Gwamnonin Arewa maso Gabas ta yi taro a Jihar Adamawa

- Kungiyar NEGF ta yi zaman da ta saba domin shawo kan matsalolinta

- Gwamna Borno, Babagana Umar Zulum ya jagoranci taron da aka yi jiya

- Jihohin Arewa maso gabas sun koka kan rashin damawa dasu a tarayya

Kungiyar gwamnonin Arewa maso gabas, NEGF, da ta kunshi jihohin Adamawa, Bauchi, Taraba, Yobe da kuma Borno sun yi taro a ranar Alhamis.

A ranar 26 ga watan Nuwamba, NEGF ta gudanar da taronta na uku, wannan karo gwamnonin yankin sun hadu ne a babban birnn jihar Adamawa.

Kamar yadda shugaban kungiyar kuma gwamnnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya bayyana, an cinma wasu matsayoyin a wajen taron.

KU KARANTA: Garkuwa da mutane: An nemi wani Mutumin Sin a Taraba an rasa

Daga cikin matsayar shi ne an samu inganci a sha’anin tsaro, musamman a kan rikicin Boko Haram, amma kuma ana fama da wasu ‘yan bindiga.

Ko da ana ganin bayan ‘yan Boko Haram, NEGF ta ce sai jami’an tsaro da al’umma sun kara kokari wajen maganin miyagun da suke garkuwa da mutane.

Kungiyar ta koka ganin yadda cewa Naira biliyan N45.3b kawai aka ware a kasafin kudin 2021 domin yin ayyukan more rayuwa a duka jihohin yankin.

NEGF ta ce ma’aikatar gidaje da ayyuka ba ta yi mata adalci a kasafi don haka ta nemi ‘yan majalisarta su sa baki a kara 0.35% da aka ware wa yankin.

KU KARANTA: Yajin-aiki: Gwamnatin Buhari ta raba hankalin ASUU

NEGF: Kungiyar Gwamnonin Arewa maso Gabas ta yi taro a Jihar Adamawa
Gwamnonin Arewa maso Gabas a Yola Hoto: GovBorno
Source: Twitter

Haka zalika NEGF tana so ayi rabon tallafin COVID-19 tsakanin yankunan kasar daidai wadaida.

A wannan taro da aka yi, NEDC ta yarda cewa sha’anin ilmi ya na cikin mawuyacin hali a yankin, ta kuma ayyana matakan da za a dauka domin ayi gyara.

Za a gudanar da taro nag aba ne a ranar 3-4 na watan Maris a Bauchi inji Babagana Umara Zulum.

A makon nan mai-ci mu ka ji majalisar dattawa ta amince da bukatar shugaba Muhammadu Buhari na biyan wasu jihohi kudin ayyukan da su ka yi.

Jihohin da Sanatoci suka amince a biya bashin sune: Bayelsa, Cross River, Ondo, Osun, da Ribas.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng News

Online view pixel