Akwa Ibom: An auka ofishin CPS, an sace wasu tulin kudi a gidan Gwamnati

Akwa Ibom: An auka ofishin CPS, an sace wasu tulin kudi a gidan Gwamnati

- Barayi sun sake fasa ofis a gidan gwamnatin Jihar Akwa Ibom sun yi sata

- Ana zargin an saci wasu miliyoyin kudin da aka ware wa manema labarai

- An saci kudin ne a ofishin CPS, inda kwanakin baya aka saci talabijin uku

Ana zargin cewa wasu barayi sun shiga gidan gwamnatin jihar Akwa Ibom, sun kuma yi awon gaba da wasu kudi da ba a san adadinsu ba.

Daily Trust ta ce an ware wannan kudi ne da sun kai miliyoyin Naira domin a biya ‘yan jarida.

Jaridar tace an kutsa cikin ofishin babban sakataren yada labaran gwamnan Akwa Ibom, Ekerette Udoh, inda aka ajiye wannan kudi, aka sace su.

Wannan barayi sun samu hanyar bude sakatar ofishin sakataren yada labaran gwamna Udom Emmanuel, sai suka wawuri wadannan tulin kudi.

KU KARANTA: Hukumar Hisbah ta damke Mata 100 da Maza 70 suna yawon bara

Wani ‘dan jarida da ya ziyarci gidan gwamnatin, ya hadu da CPS, Ekerette Udoh, wanda ya ji ya na koka wa a kan wannan barna da aka je aka yi.

Ekerette Udoh yace wannan ne karon farko da aka samu wadansu sun yi irin wannan danyen-aiki, ya ce sun dade su na ajiye kudi a nan ba a sace ba.

Wata majiya tace bayan lamarin ya auku, babban jami’in tsaron gwamnan Akwa Ibom ya bukaci ganin Ekerette Udoh, inda ya yi ta yi masa tambayoyi.

"An kawo wannan kudi tun jiya da rana, amma aka ki raba wa wadanda su ka dace. Sai barawo ya zo cikin dare, ya lalata sakatar kofar, ya shiga ofishin sakataren CPS.” Inji Majiyar.

KU KARANTA: Gwamnan Ebonyi ya fadi wanda ya mara wa baya a zaben 2019

Akwa Ibom: An auka ofishin CPS, an sace wasu tulin kudi a gidan Gwamnati
An wawuri kudi a gidan gwamnati Hoto: dailytrust.com
Source: UGC

“Ba wannan ne karon farko da aka yi sata a ofishin gidan gwamnatin ba. Mun rasa talabijin kusan uku; guda a ofishin tarbar baki, guda a ofishin ‘yan jarida, guda wajen masu daukar hoto”

Majiyar tace duk abubuwan da ke faruwa, ba a taba kiran wani zama ba, ko aka sallami wani ba.

A jiya da dare ne aka shiga ofishin CPS, aka sace wasu kudi a gidan Gwamnatin Akwa Ibom. An saci kudin ne a ofishin CPS, inda kwanakin baya aka yi sata.

Dazu kun karanta rahoto cewa an gano dabarar da Abdulrasheed Maina ya yi, ya saci idon Jami’ai, ya tsere daga Najeriya bayan ya samu an ba shi beli a kotu.

Maina ya batar da kama ne, ya tsere kan babur bayan yayi wasu takardun karya na kasar waje.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel