Duk da ina PDP a zaben 2019, Buhari nayi Inji Gwamnan Jihar Ebonyi, Umahi
- Gwamna David Umahi yace Muhammadu Buhari ya yi wa aiki a zaben 2019
- A wancan lokaci gwamnan na Ebonyi yana jam’iyyar PDP, bai koma APC ba
- Gwamnan yace tun can, idanunsa na kan abin da mutanen Ebonyi zasu samu
Gwamna David Umahi ya fito karara ya bayyana cewa ya goyi bayan shugaba Muhammadu Buhari ne a zaben 2019, duk da yana jam’iyyar PDP a lokacin.
David Umahi ya bayyana haka ne wajen aza tubulin wasu gidaje da zai gina a kauyensa, Uburu. Jaridar Premium Times ta fitar da wannan rahoto a jiya.
Gwamnan yace ka da jam’iyyar PDP ta tsaya bata lokacinta wajen zarginsa da ba Muhammadu Buhari 25% na kuri’un jiharsa a zaben 2019 da ya gabata.
“Na yi shela a Kudu maso gabashin kasar nan cewa wanda yake kaunarmu za mu mara wa baya.”
KU KARANTA: Buhari ya yabi Gwamna Umahi
Gwamnan ya bayyana dalilin sauya-shekarsa, “Na shiga APC ne saboda yadda shugaban kasa yake kaunar jihar Ebonyi.”
Yace: “Idanuna kar suke, ina duba me zai kai ga mutane na.”
Umahi yace zai mika wa shugaban kasa tsarin wani ginin gidaje da yake so a yi wa jihar Ebonyi, gwamnan yana sa ran cewa Buhari ya amince da wanna aiki.
“Kun san ni dan shi. Zaku iya fadan duk abin da kuka ga dama, amma shugaban kasa yana so na, nima ina sonsa.”
KU KARANTA: Yankin Ibo ya kamata su fito da Shugaban kasa - Umahi
Mai girma gwamnan ya kuma bayyana yadda ya hana magoya bayansa da mukarrabansa maida martani ga masu sukar matakin koma wa tafiyar APC da ya yi.
A lokacin zaben 2019 kun ji yadda gwamna David Umahi yace zai karbi bakuncin shugaban kasa Muhammadu Buhari duk da yana cikin tafiyar PDP a wancan marra.
Gwamnan yace gudun a ji kunya ya sa ya tarawa Mai girma Muhammadu Buhari Jama’a a Ebonyi, har aka samu mutum 2, 000 wajen taron gangamin APC.
Umahi yana ganin cewa Gwamnatin APC ta fi ta PDP sau dubu domin Ebonyi ta fi morarta.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng