Harun Ibn-Sina ya fadi abin da ya sa Hisbah tayi ram da wasu Mabarata

Harun Ibn-Sina ya fadi abin da ya sa Hisbah tayi ram da wasu Mabarata

- Gwamnatin jihar Kano ta haramta wa mutane fita kan ttiti suna yawon bara

- Shugaban dakarun Hisbah, Malam Harun Ibn-Sina ya ce ana kama masu laifi

- Anyi ram da wasu dake wannan haramtaccen aiki, kuma ana cigaba da kame

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mutane 178 da ake zargi da laifin yin bara a cikin birnin jihar, jaridar Vanguard ta bayyana wannan.

Shugaban dakarun Hisbah, Malam Harun Ibn-Sina ya bayyana wannan a lokacin da ya yi hira da hukumar dillacin labarai na kasa watau NAN.

Da yake magana da ‘yan jarida a yau, ranar Litinin, 7 ga watan Disamba, 2020, Harun Ibn-Sina ya yi karin haske a game da jama’an da suka kama.

KU KARANTA: Mai martaba Aminu Ado Bayero ya kai wa Sarkin Oyo ziyara

Harun Ibn-Sina ya fadi abin da ya sa Hisbah ta yi ram da wasu Mabarata
Abdullahi Umar Ganduje Hoto: freedomradionig.com
Source: UGC

“An kama wadanda ake zargi da laifi ne a lungun Alu Avenue, Dan’agundi, Taludu, Unguwar Race Course, Sharada, Kofar Mazugal a cikin birni."

Daga cikin wadanda suka shiga hannun hukumar akwai mata 100 da maza 76 inji Ibn-Sina.

Gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta dauki matakin hana bara a jihar Kano, wanda wannan ya jawo surutu tsakanin masu tir da goyon-bayan tsarin.

Ya ce: “An rage bara a titi a jihar tun da hukuma ta shiga aikin neman farautar masu saba doka.”

KU KARANTA: Farashin shinkafa zai sauka daga N30, 000 zuwa N19, 000

"Hukumar za tayi kokarin ganin babu ragowar mai bara a jihar Kano nan gaba.” Harun Ibn-Sina yace gawurtattun wadanda aka kama zasu yaba wa aya zaki.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel