Gwamnatin Amurka ta cusa Najeriya a jerin kasashe marasa ‘yancin addini

Gwamnatin Amurka ta cusa Najeriya a jerin kasashe marasa ‘yancin addini

- Gwamnatin Amurka ta na zargin Najeriya da muzguna wa mutane saboda addininsu

- Amurka ta yi wa Najeriya da wasu kasashe tabon da zai iya sa a sa masu takunkumi

- Sauran kasashen dake tare da Najeriya a wannan zargin sun hada da Saudi Arabiya

Amurka ta sa Najeriya a rukunin kasashen da ake fama da barazanar yin addini. Ta ce babu cikakken ‘yancin mutum yayi addinin da yake so.

Deutsche Welle ta rahoto cewa akwai yiwuwar nan gaba kasar Amurkar ta maka takunkumi a kan Najeriya muddin abubuwa ba su sake zani ba.

A ranar Litinin, 7 ga watan Disamba, 2020 ne kasar Amurkan ta zabi Najeriya cikin kasashen da tayi wa wannan bakin-tabo na matsin lamba a Duniya.

Wannan shi ne karon farko da Amurka ta keyi wa Najeriya kallon kasar da masu addini suke fuskantar matsin lamba da barazana daga al’ummarta.

KU KARANTA: Shugabannin kasar Amurka 10 da suka gaza zarcewa a mulki

Sauran kasashen da Najeriya take tare da su a wannan sahu su ne: Sin, Saudi Arabia, da Fakistan.

Sakataren gwamnatin kasar Amurka, Mike Pompeo, ya ce Najeriya tana cikin kasashen da suke saba dokar ba kowa a Duniya damar zaben addininsa.

An kafa wannan doka da ake kira International Religious Freedom Act ne a cikin shekarar 1998.

Mike Pompeo ya yi gargadi, yace kasar ta su da gaske take yi wajen ganin an kyale kowa a Duniya ya yi addinin da ya ga dama, ba tare da tsangwama ba.

KU KARANTA: Trump ya yarda ya sha kashi a zaben 2020

Gwamnatin Amurka ta cusa Najeriya a jerin kasashe marasa ‘yancin addini
Mike Pompeo Hoto: www.dw.com
Asali: UGC

Ka da a samu wani ko wata kasa da za ta muzguna wa mutane saboda addinin da suka yi imani da shi." Mike Pompeo ya fadi wannan a shafin Twitter.

“Wannan ya nuna babu damar mutum ya yi addini. Za mu dauki mataki.” Inji Pompeo wanda ya ja-kunnen kasashen nan da bana Indiya ta fita daga cikinsu.

Ragowar kasashe da aka yi wa wannan shaida sune: Burma, Eritriya, Iran, DPRK, Tajikistan, da Turkmenistan.

Kwanakin baya kun ji cewa budurwar babban ɗan shugaban kasar Amurka Donald Trump, Kimberly Guilfoyle ta kamu da cutar nan ta Coronavirus.

Kimberly Guilfoyle wanda ta ke soyayya da Donald Trump Jr. ta tafi jihar South Dakota domin zuwa wajen wani taron surukinta ne lokacin da ta kamu.

Daga baya shi kansa shugaban kasa, Donald Trump ya yi jinyar wannan cuta ta murar mashako.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng