Ndume ya yi martani a kan kama Maina, ya sanar da matakin da ya dauka a kan cin amanarsa

Ndume ya yi martani a kan kama Maina, ya sanar da matakin da ya dauka a kan cin amanarsa

- Sanata Ali Ndume ya umarci lauyoyinsa da su fara shirye-shiryen zame shi daga zamansa a tsayayyen Maina

- Ndume ya yi kwanaki 5 a garkame sakamakon tsaya wa Maina, wanda ya tsere ya bar shi cikin tashin hankali

- Tuni aka nemo Maina, wanda ya tsere kasar Nijar kuma aka adana shi a gidan gyaran hali har sai an gama shari'ar

Ali Ndume, Sanata mai wakiltar Borno ta kudu ya umarci lauyoyinsa da su fara bin hanyoyin janye shi daga tsayayyen Abdulrasheed Maina, tsohon shugaban hukumar fansho.

Ndume ya tsaya wa Maina wanda ke gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja, inda ake zarginsa da wawurar naira biliyan 2, The Cable ta wallafa.

Ana zargin Maina ya tsere ya bar kasar tun bayan yin belinsa a watan Satumba.

Kotu ta damki Ndume, ta kuma garkame shi a gidan gyaran hali, lokacin da Maina ya ki gabatar da kansa gaban kotun.

Ndume ya yi martani a kan kama Maina, ya sanar da matakin da ya dauka a kan cin amanarsa
Ndume ya yi martani a kan kama Maina, ya sanar da matakin da ya dauka a kan cin amanarsa. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Hukumar asibiti ta damke matar makaho a kan kasa biyan N248,000

Bayan garkame Ndume na kwana 5 a gidan gyaran hali, an amince da belinsa saboda yadda yake da tarihin nagarta.

An damko Maina a kasar Nijar, inda aka dawo da shi Najeriya. A ranar Juma'a, kotu ta umarci a garkame Maina a gidan gyaran hali da ke Kuje, har a karasa shari'ar shi.

KU KARANTA: Da duminsa: Kotun daukaka kara ta jaddada hukuncin kisa a kan Maryam Sanda

A wani labari na daban, babban malamin addinin musulunci na jihar Kaduna, Dr Ahmad Abubakar Gumi, ya ce rikicin kudancin Kaduna ya dauki lokaci mai tsawo, Daily Trust ta wallafa.

A cewarsa, ya zama tilas mutanen kirki, maza da mata, su hada karfi da karfe wurin kawo karshen rikicin addinin.

Dr Gumi, wanda shine shugaban KHF ya fara shirin kawo karshen rikicin addini da ke addabar kudancin Kaduna, wanda yake hana cigaba da zaman lafiya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng