Yanzu-yanzu: Zan bude boda nan ba da dadewa ba, Buhari

Yanzu-yanzu: Zan bude boda nan ba da dadewa ba, Buhari

- Babban Albishiri ga yan Najeriya, Buhari ya bayyana abinda ya tattauna da gwamnoni

- Ya zauna da su bayan zaman majalisar zartaswar jam'iyyar All Progressives Congress APC

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba zai bude iyakokin Najeriya.

Ya bayyana hakan ga gwamnonin Najeriya 36 a ganawar da yayi da su ranar Talata, 8 ga watan Disamba, 2020.

Buhari ya ce ya rufe iyakokin ne domin hana fasa kwabrin makamai da kwayoyi amma tun da yanzu makwabtan Najeriya sun hankalta, zai iya bude wa.

Buhari ya bayyana tattaunawarsa da gwamnonin a shafinsa na Tuwita.

"A ganawa da gwamnoni yau nayi bayanin cewa an kulle iyakokin Najeriya na kasa ne domin lura da fasa kwabrin makamai da kwayoyi. Amma yanzu da sakon ya isa ga kunnawan makwabtanmu, muna tunanin budewa nan ba da dadewa ba," Buhari yace.

KU KARANTA: Jam’iyyar PDP ta nemi a kashe APC saboda ta sauke daukacin Shugabanninta

Yanzu-yanzu: Zan bude boda nan ba da dadewa ba, Buhari
Yanzu-yanzu: Zan bude boda nan ba da dadewa ba, Buhari
Source: UGC

Mun kawo muku rahoton cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga ganawar sirri tare da dukkanin gwanonin jihohi 36.

Sun yi ganawar ne a fadar Shugaban kasa da ke Abuja a yau Talata, 8 ga watan Disamba.

Ganawar tasu na zuwa ne bayan kungiyar gwamnonin kasar sun gana a makon da ya gabata tare da Shugaban kasar kan halin da lamarin tsaro ke ciki.

KU KARANTA: EFCC ta gayyaci tsohon gwamnan Kwara Abdulfatah Ahmed domin ya amsa tambayoyi

A ranar 25 ga Nuwamba, 2020, mun kawo muku cewa Ministar ta kudi Zainab Shamsuna ta ce kwamitin da shugaba Buhari ya nada don duba ribar rufe iyakokin sun bashi shawaran cewa ya bude.

Saboda haka, tana kyautata zaton cewa Buhari zai dauki shawarar kuma ya aiwatar nan ba da dadewa ba.

Duk da cewa bata bayyana takamammen ranan da za'a bude ba, amma ko shakka babu tace za'a bude nan ba da dadewa ba

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel