Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari na cikin ganawa da dukka gwamnonin Nigeria 36

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari na cikin ganawa da dukka gwamnonin Nigeria 36

- Shugaba Muhammadu Buhari ya shiga labule da gwamnonin kasar 36

- Sun shiga ganawar ne a fadar villa a ranar Talata, 8 ga watan Disamba

- Zuwa yanzu babu wani cikakken bayani game da ganawar tasu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari na cikin ganawar sirri tare da dukkanin gwanonin jihohi 36 a yanzu haka.

Suna ganawar ne a fadar Shugaban kasa da ke Abuja a yau Talata, 8 ga watan Disamba, Channels Television ta ruwaito.

Ganawar tasu na zuwa ne bayan kungiyar gwamnonin kasar sun gana a makon da ya gabata tare da Shugaban kasar kan halin da lamarin tsaro ke ciki.

KU KARANTA KUMA: EFCC ta gayyaci tsohon gwamnan Kwara Abdulfatah Ahmed domin ya amsa tambayoyi

A gefe guda Legit.ng ta tattaro cewa gwamnonin jihohi 36 na kasar nan a karkashin kungiyar NGF za su zauna a gobe, 2 ga watan Disamba, 2020, a dalilin sha’anin tsaro.

Babban makasudin wannan taro shi ne gwamnonin su fito da sabon tsari a game da harkar tsaro.

A halin yanzu ana fama da yawan hare-haren ‘yan bindiga, ta’addancin Boko Haram da garkuwa da mutane da ake yi a jihohi da-dama a Najeriya.

KU KARANTRA KUMA: APC ta kori tsohon mataimakin Oshiomhole, ta rushe shugabancin shiyya da jihohi

A wani labarin kuma, mun ji cewa kungiyar sa Ido kan hakkin dan adam (SERAP) na shirin shigar da kara a kan Shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnonin Najeriya kan bukatar karbo bashi daga kudaden fansho.

Legit.ng ta tattaro cewa kungiyar ta yi wannan sanarwar ne a cikin wani wallafa da tayi a shafin Twitter a ranar Litinin, 7 ga watan Disamba.

SERAP ta kuma bukaci yan Najeriya da su nuna ra’ayinsu ta hanyar bayyana cikakken sunayensu domin shiga sahun masu kara wanda za a shigar nan da kwanaki 14.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel