Jam’iyyar PDP ta nemi a kashe APC saboda ta sauke daukacin Shugabanninta

Jam’iyyar PDP ta nemi a kashe APC saboda ta sauke daukacin Shugabanninta

- PDP tayi kira ga hukumar INEC ta soke rajistar da aka yi wa APC tun 2013

- Jam’iyyar hamayyar tace tun da aka sauke shugabannin PDP, ta tashi aiki

- Dazu nan ne APC ta sauke shugabanninta da ke fadin Najeriya a taron NEC

Yanzu nan mu ke jin cewa jam’iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta yi kira ga hukumar zabe na kasa watau INEC ta soke rajistar da aka ba APC.

Jam’iyyar hamayyar tayi wannan kira ne jim kadan bayan APC ta dauki matakin rusa daukacin shugabanninta da ke kasa, shiyyoyi da kuma jihohi.

Sakataren yada labaran PDP, Kola Ologbondiyan, ya fitar da jawabi jim kadan bayan APC ta sauke shugabanninta, ya fito yana taya ‘Yan Najeriya murna.

KU KARANTA: An kori Eta daga APC

Mista Kola Ologbondiyan yace da wannan mataki da jam’iyyar APC mai mulki ta dauka, ta yi waje da kanta da kanta daga cikin jam’iyyun siyasa.

A cewar Kola Ologbondiyan, jam’iyyar APC tana bukatar shugabanni a duka bangarorin kasar nan kafin ta amsa sunanta na zama jam’iyya a doka.

Jam’iyyar adawar ta bukaci INEC ta shirya sababbin zabuka domin a cike guraben kujerun APC.

“INEC tayi gaggawar bayyana cewa APC bata da kujerar majalisa a tarayya da jihohi, ta fara shirin zaben cika-gurbi kamar yadda dokar kasa ta tanada.”

KU KARANTA: Buhari yana taro da Gwamnoni

Jam’iyyar PDP ta nemi a kashe APC saboda ta sauke daukacin Shugabanninta
Taron Jam’iyyar APC Hoto: Legit.ng
Source: Twitter

Mai magana da yawun PDP yake cewa: “Bayan haka, hukumomin gwamnati, kungiyoyi masu zaman kansu, da kasashen ketare su cire APC daga lissafinsu.”

“Bayan haka PDP tana kira ga duka shugabannin APC da aka ruguza, su amsa laifuffukansu, su daina tunanin za a manta ta’adinsu idan sun sauya-sheka.”

A taron na dazu kun ji cewa an tsawaita wa'adin kwamitin rikon kwaryan uwar jam'iyyar APC da ke karkashin Mai Mala Buni, za a yi zabe a tsakiyar 2021.

Hakan na zuwa ne a lokacin da aka sallami tsohon mataimakin Adams Oshiomole, Hilliard Eta, wanda ya shigar da karar jam'iyya a kotu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel