Yanzu-yanzu: An sauke dukkan shugabannin jam'iyyar APC a fadin tarayya

Yanzu-yanzu: An sauke dukkan shugabannin jam'iyyar APC a fadin tarayya

- An tsawaita wa'adin kwamitin rikon kwaryan uwar jam'iyyar APC karkashin Buni

- An sallami tsohon mataimakin Oshiomole, Hilliard Eta, wanda ya shigar da jam'iyyar kotu

- Za'a shirya taron gangamin jam'iyyar nan da watanni shida

Majalisar zartaswa, NEC, na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta sauke dukkan shugabannin jam'iyya na dukkan matakai a fadin tarayya.

Wannan ya hada da shugabannin jam'iyyar na jihohi, yankuna da kasa.

Thisday ta ruwaito cewa gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i ya bayyana hakan yayin hira da manema labarai a fadar shugaban kasa bayan ganawar majalisar ranar Talata.

El-Rufa'i ya sanar da hakan ne tare da takwarorinsa na Imo da Ondo, gwamna Hope Uzodinma, da gwamna Rotimi Akeredolu.

KU KARANTA: Dan majalisa, Hernan Hembe, ya sauya sheka jam'iyyar APC

Yanzu-yanzu: An sauke dukkan shugabannin jam'iyyar APC a fadin tarayya
Yanzu-yanzu: An sauke dukkan shugabannin jam'iyyar APC a fadin tarayya @BashirAhmaad
Asali: Twitter

A bangare guda, kwamitin zartarwa na jam'iyyar APC (NEC), a ranar Talata, ya sanar da korar tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar mai kula da shiyyar kudu maso kudu, Ntufam Hilliard Eta.

Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufa'i, ne ya tabbatar da korar ita yayin tattaunawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron.

Hakazalika, an tsawaita wa'adin kwamitin rikon kwarya karkashin jagorancin gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni.

An tsawaita wa'adin zuwa ranar 30 ga Yunin 2021.

KU DUBA: Rashin Tsaro: Wani mutumin Katsina ya canza sunansa daga Buhari

Mun kawo muku cewa majalisar zartaswar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) tayi zaman gaggawa a fadar shugaban kasa, Aso Villa, yau Talata

Za ku tuna jam'iyyar ta shirya zaman a watan Nuwamba domin sanin abin yi kan shugabancinta amma bata samu dama ba.

Shugaban kwamitin rikon kwaryar jam'iyyar kuma gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya jagoranci sauran mambobin majalisar zartaswar, har da shugaba Buhari wajen bude taron.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng