Kudin Fansho: SERAP za ta maka Buhari da gwamnonin jihohi 36 a gaban kotu kan bashi

Kudin Fansho: SERAP za ta maka Buhari da gwamnonin jihohi 36 a gaban kotu kan bashi

- Ana shirin kai Shugaban kasa Muhammadu Buhari gaban kotu kan bukatar da gwamnonin jihohi suka gabatar na ciyo bashi

- Kungiyar SERAP ce za ta maka Shugaban Najeriyan da gwamnonin jihohi 36 a gaban kotun

- A cewar SERAP, bukatar gwamnonin na ciyo bashi daga kudaden fansho ya saba doka

Kungiyar sa Ido kan hakkin dan adam (SERAP) na shirin shigar da kara a kan Shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnonin Najeriya kan bukatar karbo bashi daga kudaden fansho.

Legit.ng ta tattaro cewa kungiyar ta yi wannan sanarwar ne a cikin wani wallafa da tayi a shafin Twitter a ranar Litinin, 7 ga watan Disamba.

SERAP ta kuma bukaci yan Najeriya da su nuna ra’ayinsu ta hanyar bayyana cikakken sunayensu domin shiga sahun masu kara wanda za a shigar nan da kwanaki 14.

Kudin Fansho: SERAP za ta maka Buhari da gwamnonin jihohi 36 a gaban kotu kan bashi
Kudin Fansho: SERAP za ta maka Buhari da gwamnonin jihohi 36 a gaban kotu kan bashi Hoto: @NigeriaGov
Asali: Twitter

Wannan ci gaban na zuwa ne yan sa’o’i bayan SERAP ta bukaci shugaba Buhari da ya dakatar da gwamnonin jihohin daga daukar bashi daga asusun fansho.

KU KARANTA KUMA: Yan Najeriya sun caccaki Zulum kan cewa da yayi tsaro ya inganta a Borno karkashin Buhari

Kungiyar a shafinta na Twitter a ranar Lahasi, 6 ga watan Disamba, ta bukaci Shugaban kasar a kan yayi gaggawan umurtan darakta janar da hukumar fasho ta kasa kan su dakatar da yunkurin gwamnonin.

Ta wallafa cewa:

"Da dumi-dumi: Muna shirya takardun kotu don maka Shugaban kasa Buhari da gwamnonin jihohi 36 a gabanta kan bukatar gwamnoni na ranto kudi daga asusun fansho wanda baya bisa ka’ida. Dan Allah ku nuna ra’ayinku na shiga karar (wanda za a shigar nan da kwanaki 14) a matsayin masu kara ta hanyar bayyana cikakken sunayenku.”

KU KARANTA KUMA: Buhari zai yi jawabi ga majalisar dokokin tarayya a ranar Alhamis, 10 ga watan Disamba

A wani labarin, mai girma gwamnan Jigawa ya bayyana cewa jiharsa ta karbi wasu kudinta da ta ke jira daga hannun gwamnatin tarayyar Najeriya.

The Nation ta rahoto cewa Muhammadu Badaru Abubakar ya tabbatar da karbar fiye da Naira biliyan 47 daga hannun gwamnatin tarayya.

Gwamna Muhammadu Badaru Abubakar yace an dawo masu da wannan kudi ne saboda abin da gwamnatin jiha ta kashe wajen gina filin jirgi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel