Ifeanyi Ararume yace ba APC Hope Uzodinma yayi wa aiki a zaben da aka yi ba

Ifeanyi Ararume yace ba APC Hope Uzodinma yayi wa aiki a zaben da aka yi ba

- Ifeanyi Araraume ya kai karar Gwamna Hope Uzodinma gaban manyan APC

- Sanata Ifeanyi Araraume ya zargi Gwamnan Imo da yi wa Jam’iyyar PDP aiki

- Bayan haka mun ji cewa masu shara suna zanga-zangar rashin albashi a jihar

Tsohon sanata, Ifeanyi Araraume, ya zargi gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, da yi wa jam’iyyarsa ta APC makarkashiya a zabukan yankin Kudu.

Sanata Ifeanyi Araraume wanda yake ikirarin shi ne ‘dan takarar APC a zaben Imo ta Arewa da aka yi kwanan nan, ya bada shawarar a ja-kunnen gwamnan.

Punch ta ce tsohon ‘dan majalisar ya jefi Mai girma Hope Uzodinma da wannan zargi na zagon-kasa ne lokacin da ya tattauna da manema labarai ranar Lahadi.

A cewarsa, gwamnan ya ba ‘ya ‘yan APC umarni suyi wa PDP aiki a zaben cike gurbin da aka yi. Araraume yace tun farko ‘yan adawa ake ba mukamai a Imo.

KU KARANTA: Tsohon Gwamnan PDP ya tona kan sa da kan sa, Buhari yayi a 2019

Sanata Ifeanyi Araraume ya ke cewa gwamna Uzodinma ya yi duk yadda zai iya wajen ganin ya kawo masa matsala, amma a karshe jam’iyyar APC ta ci zabe.

Ararume ya caccaki gwamnan a game da ja da ya yi da hukuncin da babban kotun tarayya ta yi.

Gwamnan ya maida martani ta bakin wani hadiminsa, Modestus Nwamkpa, wanda yace karyar banza ce kurum Ararume yake yi, yace mai gidansa su ne APC.

A daidai wannan lokaci ne kuma mu ka ji cewa masu aikin share-share a jihar Imo sun tare kofar shiga gidan gwamnati a Owerri, domin nuna wa gwamna fushinsu.

KU KARANTA: AYCC tana so Buhari ya tsige Hafsoshin tsaro da Ministan ayyuka

Ifeanyi Ararume yace ba APC Hope Uzodinma yayi wa aiki a zaben da aka yi ba
Gwamna Hope Uzodinma Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Ma’aikatan sun shirya zanga-zanga har ofishin gwamna saboda albashin da aka hana su. Masu sharar suka ce tun da Uzodinma ya hau mulki, ba a taba biyansu ba.

A ranar Lahadi kun ji cewa gwamnatin tarayya da mai girma Muhammadu Buhari yake jagoranta, ta maida wa Jihar Jigawa wasu makudan Biliyoyi da ta ke jira.

Gwamnan Jigawa, Badaru Abubakar ya tabbatar da cewa an biya su bashin Paris Club da su ke bi. Wadannan kudi da su ka shigo asusun jihar sun haura Naira biliyan 47.

Sannan gwamnati ta ba Jigawa abin da ta kashe wajen gina filin jirgin sama da ke garin Dutse.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel