Buhari zai yi jawabi ga majalisar dokokin tarayya a ranar Alhamis, 10 ga watan Disamba

Buhari zai yi jawabi ga majalisar dokokin tarayya a ranar Alhamis, 10 ga watan Disamba

- Yan Najeriya na gab da jin jawabi daga Shugaban kasa Muhammadu Buhari

- Shugaban kasar ya amince zai yi jawabi ga majalisar dokokin tarayya kan halin da tsaron kasar ke ciki

- Hadimar Shugaban kasa, Lauretta Onochie ce ta sanar da hakan a Twitter

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi jawabi daga karshe a kan lamuran tsaro a cikin kasar.

Kan haka, Buhari zai yi jawabi ga majalisun dokokin tarayya biyu a ranar Alhamis, 10 ga watan Disamba.

Shugaban kasar zai sanar da kasar matakan da yake dauka domin dakatar da ci gaban kashe-kashe, garkuwa da mutane da sauran miyagun ayyuka.

Buhari zai yi jawabi ga majalisar dokokin tarayya a ranar Alhamis, 10 ga watan Disamba
Buhari zai yi jawabi ga majalisar dokokin tarayya a ranar Alhamis, 10 ga watan Disamba Hoto: @Laurestar
Asali: Twitter

Hadimar Shugaban kasa, Lauretta Onochie ce ta sanar da hakan a wani wallafa da tayi a shafin Twitter a ranar Litinin, 7 ga watan Disamba.

KU KARANTA KUMA: Duniya labari: Budurwa ƴar Arewa ta roƙi mahaifin ta yayi mata aure, ko na dole ne

Ku tuna cewa a kwanan ne majalisar wakilai ta gayyaci Buhari kan ya gurfana a zaurenta.

Hakan ya biyo bayan kisan manoma a jihar Borno wanda mayakan Boko Haram suka yi.

Hakazalika, majalisar dattawa ma ta bukaci Buhari ya sallami shugabannin tsaronsa.

Legit.ng ta kawo a baya cewa majalisar wakilai ta yi watsi da bukatar wani dan majalisa na neman a tsige Shugaban kasa Muhammadu Buhari daga kujerar mulki.

Dan majalisa mai wakiltan mazabar Obio/Akpor ta Jihar Rivers, Kingsley Chinda shine yayi wannan kira, inda ya bukaci yan Najeriya da su matsa lamba don ganin wakilansu a majalisar sun fara shirin tsige shugaban kasar a ranar Lahadi.

KU KARANTA KUMA: Mazan Hausawa su rinƙa auren mata fiye da 1, budurwa ta koka da rashin samari

Mai magana da yawun majalisar, Benjamin Kalu a ranar Litinin, 7 ga watan Disamba, ya ce kiran da dan majalisar na Peoples Democratic Party (PDP) yayi baya bisa ka’ida.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel