Yan Najeriya sun caccaki Zulum kan cewa da yayi tsaro ya inganta a Borno karkashin Buhari

Yan Najeriya sun caccaki Zulum kan cewa da yayi tsaro ya inganta a Borno karkashin Buhari

- Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya sha caccaka a shafin soshiyal midiya

- Furucin Zulum game da lamarin tsaro a Borno ya jawo masa suka daga yan Najeriya da dama

- An tattaro cewa gwamnan ya ce lamarin tsaro a Borno ya inganta sosai a karkashin Buhari

Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, a ranar Lahadi, 6 ga watan Disamba ya ce duk da kisan akalla manoman shinkafa 43 da mayakan Boko Haram suka yi kwanan nan, lamarin tsaro ya inganta a jihar karkashin gwamnatin Buhari.

Gwamnan ya yi wannan furucin ne a Maiduguri, babbar birnin jihar Borno lokacin da ya karbi bakuncin dattawan arewa karkashin jagorancin babban jigon kungiyar, Ambassador Shehu Malami, da Shugaban kungiyar, Audu Ogbeh.

A wata sanarwa daga gwamnatin jihar Borno wanda Legit.ng ta gano, gwamnan ya ce:

“Daga bayanai da mu ka samu daga kananan hukumomi 27 na jihar Borno tun daga shekarar 2011, shaidu sun nuna cewa duk da irin kashe-kashen da ke faruwa a Borno, an samu ingantuwar zaman lafiya a Borno da yankin arewa maso gabas, mu na da shaidu a kan hakan.”

Yan Najeriya sun caccaki Zulum kan cewa da yayi tsaro ya inganta a Borno karkashin Buhari
Yan Najeriya sun caccaki Zulum kan cewa da yayi tsaro ya inganta a Borno karkashin Buhari Hoto: @PremiumTimesng
Source: Twitter

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari yayi gagarumin gargadi yayinda masu zanga zangar EndSARS suka sake fitowa unguwanni

Wannan furuci na gwamnan ya janyo cece-kuce sosai daga yan Najeriya a shafin soshiyal midiya, inda mutane da dama suka kira gwamnan a matsayin munafiki kan matsayarsa.

Wasu kuma sun zargi gwamnan na Borno da buga wasan siyasa da lamarin tsaro a yankinsa, maimakon fadawa masu rike da madafin iko gaskiya.

Wasu kuma na ganin kawai dai gwamnan yana taka-tsan-tsan ne, don kada ya bata dangantakarsa da gwamnatin tarayya.

Chijiоke Ekwulu ya wallafa a Twitter:

“Farfesa Zulum, na son yan Najeriya masu hikima su yarda cewa lamarin tsaro a jiharsa ya inganta a karkashin Buhari. Wannan ne karo na karshe da zan sake tattauna wani batu kan lamarin tsaro a jihar Borno. Ba zan iya kuka sama da wanda abun ya shafa ba.”

Judith Saleh ya rubuta:

“Na fara tunanin, wadannan hare-haren da ake kai wa Zulum an shirya su ne don yin suna.”

Sodiq Tade ya rubuta:

“Masari zai koka rashin tsaro, ya koma Katsina ya sasanta da yan bindiga, sannan ya jinjinawa Buhari a kan shugabanci na gari. Zulum zai yi gudu zuwa wajen da al’amarin ta’addanci ya wakana, ya wallafa hotunan ban tausayi daya zuwa biyu da gawawwaki, sannan kuma ya koma kafofin watsa labarai yana yabawa Buhari.”

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An dawo da zanga zangar #EndSARS a garin Osogbo

Umar Sa'ad Hassan ya rubuta:

“Zulum ya kasance daya daga cikin gwamnoni masu aiki a arewa. El Rufai ma haka. Yayinda cikin sauki za a gane kuskuren El Rufai cikin sauki a matsayin makiri (nuna biyayya a ko ina), Zulum ma ya kasance dan kashenin Buhari ko da kuwa zai saka mutanensa cikin hartsari. Dukkaninsu su biyu basu zamo shugabannin da ake muradi ba."

A gefe guda, Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi jawabi daga karshe a kan lamuran tsaro a cikin kasar.

Kan haka, Buhari zai yi jawabi ga majalisun dokokin tarayya biyu a ranar Alhamis, 10 ga watan Disamba.

Shugaban kasar zai sanar da kasar matakan da yake dauka domin dakatar da ci gaban kashe-kashe, garkuwa da mutane da sauran miyagun ayyuka.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel