Yanzu Yanzu: Buhari yayi gagarumin gargadi yayinda masu zanga zangar EndSARS suka sake fitowa unguwanni
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi jan kunne yayinda masu zanga zangar EndSARS suka koma tituna don yin gangami
- Buhari ya ce lallai za a dauki mummunan mataki kan bata-garin da za su yi amfani da damar wannan zanga zanga ta lumana wajen yin ta'asa
- A yau Litinin, 7 ga watan Disamba ne dai wasu matasa suka dawo da yin tattaki a kasar
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kakkausar gargadin cewa za a dauki mummunan mataki a kan duk wani ta’asa da wasu za su aikata da sunan zanga zanga.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da fadar Shugaban kasa ta saki a ranar Litinin, 7 ga watan Disamba, a shafinta na Facebook.
KU KARANTA KUMA: NSCDC ta ceto wata mata da yan uwanta suka kulle ta tsawon watanni 5 a daki
Takaitacciyar sanarwar ta zo kamar haka:
“Shugaban kasa Muhammadu Buhari a yau a Abuja ya yi gargadin cewa za a dauki mummunan mataki a kan duk wani mugun aiki da za a yi ta hanyar fakewa a karkashin zanga zangar lumana da ke bisa doka domin tabbatar da zaman lafiya da daidaituwar lamura a kasar.”
A baya mun ji cewa, biyo bayan tsoro da ake yi na barkewar sabuwar zanga-zangar EndSARS, an tura jami’an yan sanda da na sojoji zuwa mashigin harabar Lekki Toll Gate.
Masu ababen hawa da masu tafiya a kafa sun sanar da manema labarai cewa an zuba jami’an tsaro a wajen a safiyar ranar Litinin, 7 ga watan Disamba.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An dawo da zanga zangar #EndSARS a garin Osogbo
Sai dai jaridar Punch ta ruwaito cewa jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sanda, Muyiwa Adejobi, ya ki amsa kiran wayar da aka yi masa a safiyar yau Litinin.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng