Budurwar Trump ta kamu da cutar korona
Budurwar babban ɗan shugaban Amurka Donald Trump ta kamu da coronavirus kamar yadda kafafen watsa labarai na ƙasar suka ruwaito a ranar Juma'a.
Kimberly Guilfoyle, tsohuwar mai gabatar da shirye-shirye a gidan talabijin na Fox na soyayya da Donald Trump Jr.
Ta tafi jihar South Dakota domin zuwa sauraron jawabin shugaban ƙasa na ranar 'Fourth of July' da shagalin da aka yi a Mount Rushmore kamar yadda The Punch ta ruwaito.
New York Times ta ruwaito cewa an killace Guilfoyle mai shekaru 51 nan take bayan an gano ta kamu da cutar ta Coronavirus yayin gwajin da ake yi wa dukkan wadanda ake sa ran za su kusanci shugaban ƙasa.
KU KARANTA: Zaben Edo: APC ta tura Ganduje, PDP ta tura Wike
Wata sanarwa da Shugaban ma'aikatan kwamitin Kuɗi na yakin neman zaben Trump, Sergio Gor ya aike wa jaridu ta ce, "Tana cikin ƙoshin lafiya a yanzu, za a sake mata gwaji a tabbatar ba kuskure bane duba da cewa ba ta da alamun cutar."
Ya ƙara da cewa, "Don ɗaukan matakin tsaro, ba za ta gana da kowa ba. Donald Trump Jnr bai kamu da cutar ba amma saboda tsaro shima ya killace kansa."
Guilfoyle ita ce mutum na uku na kusa da shugaban na Amurka da gwaji ya nuna sun kamu da ƙwayar cutar ta coronavirus kamar yadda kafafen watsa labaran Amurka suka ruwaito.
Sauran sun haɗa da mai bawa shugaban kasar abinci da sakataren watsa labaran mataimakin shugaban kasar.
Annobar ta coronavirus ta kashe kimanin mutum 130,000 a Amurka kuma akwai alamun annobar na sake dawowa karo na biyu.
Hakan ka iya jefa ƙasar cikin babban hatsari a cewar babban ƙwararre a fanin cututtuka masu ƴaduwa na kasar Anthony Fauci.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng