Gudun a ji kunya ya sa na tarawa Buhari Jama’a a Ebonyi – inji Umahi

Gudun a ji kunya ya sa na tarawa Buhari Jama’a a Ebonyi – inji Umahi

Mun ji cewa Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi ya bayyana ainihin dalilin da ya sa ya tara har mutum 2,000 su ka halarci gangamin yakin neman zaben shugaba Muhammadu Buhari a jihar sa.

Gudun a ji kunya ya sa na tarawa Buhari Jama’a a Ebonyi – inji Umahi

Umahi yace Buhari zai samu kuri'un da su ka dara na 2015 a bana
Source: UGC

Mai girma gwamnan ya bayyana wannan ne jim bayan shugaban kasa Buhari ya bar jihar Ebonyi a makon da ya gabata. Gwamna Umahi yake cewa idan har jama’a ba su halarci taron ba, Buhari zai ji cewa jama’a ba su son sa.

Gwamna Umahi yace saboda gudun jama’a su kauracewa filin wasan da aka shirya taron yakin neman zaben APC ne ya tara jama’a har kimanin 2, 000 domin su fito su nuna farin cikin su a zahiri na ganin shugaban kasa a jihar su.

KU KARANTA: Har a Adamawa Atiku sai ya sha kashi a hannun APC - Masoyan Buhari

Mai girma gwamnan ya fadawa jaridar Daily Sun cewa sai da yayi wa filin wasan da Buhari yayi taro kwaskwarima da wasu gyare-gyare domin kurum Buhari ya ji dadi. Gwamnan yace bai dauki bakar gaba ya sa a harkar siyasar sa ba.

Mista Umahi yake cewa ya tara jama’a ne kurum saboda ganin mutuncin shugaban kasa inda yace idan aka lura jama’an da ya tara ko kadan ba su tare da Buhari. Umahi ya kuma ce asali bai kamata a gan sa tare da Buhari wajen kamfe ba.

Shugaban gwamnonin na Kudu maso gabashin Najeriya ya nuna cewa babu shakka Buhari zai samu kuri’un da su ka dara abin da ya samu a lokacin zaben 2015 inda PDP tayi wa jam'iyyar APC raga-raga.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel