Buhari: Da mutane kamar Umahi, ina hangen kyakkyawar makomar dimokradiyya

Buhari: Da mutane kamar Umahi, ina hangen kyakkyawar makomar dimokradiyya

- Shugaba Muhammadu Buhari ya yabi Gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi bisa barin PDP ya shigo APC

- Buhari ya ce sauya sheƙar da Umahi ya yi don ƙashin kansa ya bashi ƙwarin gwiwar cewa dimokuraɗiyya zata inganta

- Shugaban ƙasar kuma ya nuna farin cikinsa bisan shigowar Umahi APC tare da yaba wa jarumtarsa

Shugaba Muhammadu Buhari ya yabawa David Umahi, gwamnan Ebonyi, saboda chanja sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC.

A ranar Talata, Umahi ya bayyana komawa APC, yana mai cewa ya bar tsohuwar jam'iyyar sa saboda rashin adalci.

Buhari: Da mutane kamar Umahi, ina hangen kyakkyawar makomar dimokradiyya
Buhari: Da mutane kamar Umahi, ina hangen kyakkyawar makomar dimokradiyya. Hoto: @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

A wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa, ya nuna yadda Buhari ya yabi Umahi.

DUBA WANNAN: 'Na gwammace a datse min kai a maimakon in bada haƙuri', martanin Bashir El Rufai ga masu sukar hotunansa da Nwakaego

An ruwaito cewa Buhari ya bayyana chanjin shekar "a matsayin canjin da ya dace, bawai saboda neman wata dama ba."

"Ina alfahari da Gwamna David Umahi da ya yanke wannan shawara bisa ra'ayin kansa ba tare da matsawa ko tursasawar wani ba," a bayanin shugaban ƙasar.

"Kyakkyawan shugabanci yana da matukar amfani anan APC, kuma naji dadi da gwamnan yayi la'akari da wannan kafin dawowa cikin mu. Ina shawartar al'umma da su daina siyasar sanayya matukar muna so dimokradiyya ta kawo mana kyakkyawan cigaba a ƙasarmu.

KU KARANTA: Gobara ta lashe gidan man fetur da shaguna 30 a kasuwa

"Da mutane kamar Umahi, ina hango kyakkyawar makomar dimokradiyya saboda masu zabe zasu samu ƙwarin gwiwa daga irin ayyukan da jam'iyya da yan takara.

"Bari in kara yabawa jarumtar Umahi na yanke wannan kyakkyawar shawara a kasa wadda irin wannan kewa al'umma da dama wahala."

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, gwamnatin Jihar Kogi za ta bullo da sabon haraji a kan kowanne gasashen burodi a jihar kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Ma'aikatar kasuwanci da masana'antun tace harajin zai taimaka wajen kara samun kudaden shigar da ake samu na cikin gida.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164