Gwamnan Nasarawa ya ziyarci Borno, ya je da muhimmiyar bukata 1
- Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya ce ya kamata a canja salon yakar 'yan ta'adda
- Gwamnan ya fadi hakan ne yayin da shi da sarakunan jiharsa suka kai wa Gwamna Zulum Ziyara
- Sule ya ce tun da dabarun da ake yin amfani dasu sun ki yin aiki, ya kamata a dubi wasu na daban
Gwamnan jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi A. Sule, ya ce wajibi ne a fuskanci ta'addanci gaba da gaba sannan a canja salo idan dabarun da aka yi amfani dasu sun ki yin aiki.
Gwamnan ya fadi hakan ne a ranakun karshen mako, lokacin da ya jagoranci wata ziyara tare da tsohon gwamnan jihar, Sanata Umar Tanko AlMakura; Sarkin Lafiya, Justice Sidi Bage Mohammed; Sarkin Keffi, Dr Shehu Chindo Mohammed II da Sanata John Danboye don ta'aziyya ga gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, a kan kisan manoman Zabarmari a Maiduguri.
"Za mu yi amfani da wannan damar don kira ga duk shugabanninmu, har da shugaban kasa, a kan yadda za mu fara tunanin canja salo tunda mun yi amfani da dabaru iri-iri.
KU KARANTA: Tirkashi: APC ta lashe kujerar sanatan Imo amma babu takamaiman dan takara
"Idan dabarunmu ba su yi aiki ba, babu laifi idan mun canja salo, matukar za mu samu nasara," a cewarsa.
Haka nan kuma Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdurrazaq ya je yi wa Zulum jaje a Maiduguri a kan kisan manoman Zabarmari.
Gwamna Zulum ya bayyana musu farincikinsa a kan yadda suka nuna kula har suka kai masa ziyara don jaje, Daily Trust ta wallafa.
KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: Maryam Sanda ta garzaya kotun koli domin kalubalantar hukuncin kisa
A wani labari na daban, babbar kotun tarayya da ke jihar Legas ta amince wa tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, wanda ake zargin damfarar naira biliyan 2.2, ya tafi kasar waje neman lafiya.
Mai shari'a Chukwujekwu Aneke ya amince da bukatar da lauyansa, Ola Olanipekun (SAN), wanda ya bukaci kotu ta amince yayi tafiyar.
EFCC, ta lauyanta Rotimi Jacobs (SAN), bai kalubalanci bukatar Fayose ba, Channels TV ta wallafa hakan.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng