Bidiyon dakarun sojin sama suna ragargaza 'yan bindiga a dajin Kuduru da ke Kaduna

Bidiyon dakarun sojin sama suna ragargaza 'yan bindiga a dajin Kuduru da ke Kaduna

- Rundunar sojin sama ta Operation Thunder Strike ta samu nasarar ragargazar 'yan ta'adda a Kaduna

- Sun samu nasarar kashe fiye da 'yan ta'adda 10, tare da lalata maboyarsu da ke dajin Kuduru a ranar Asabar

- Kakakin rundunar sojin, Manjo janar John Enenche ya sanar da hakan a wata takarda da ya fitar

Hedkwatar tsaro ta ce rundunar sojin sama ta Operation Thunder Strike, sun samu nasarar ragargazar 'yan ta'adda a sansaninsu da ke wuraren dajin Kuduru dake jihar Kaduna a ranar Asabar.

Kakakin rundunar soji, Manjo janar John Enenche, ya sanar da hakan a wata takarda, inda yace rundunar ta yi amfani da dabara ta musamman wurin kai hari ga 'yan ta'addan.

Fiye da 'yan bindiga 10 sojojin suka kashe a dajin, inda suka yi amfani da ISR wurin gano maboyar tasu.

Kamar yadda yace, rundunar sun samu nasarar yin raga-raga da maboyar 'yan ta'addan, daga nan ne suka samu nasarar kashe 'yan ta'adda da dama.

Bidiyon dakarun sojin sama suna ragargaza 'yan bindiga a dajin Kuduru da ke Kaduna
Bidiyon dakarun sojin sama suna ragargaza 'yan bindiga a dajin Kuduru da ke Kaduna. Hoto daga @DefenceInfoNG
Asali: UGC

Hedkwatar tsaro ta wallafa bidiyon yadda lamarin ya kasance.

KU KARANTA: Ndume ya yi martani a kan kama Maina, ya sanar da matakin da ya dauka a kan cin amanarsa

KU KARANTA: Hotuna da bidiyon ziyarar da Sarki Bayero ya kai wa Gwamna Sanwo-Olu

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu, ya dakatar da shugaban ma'aikatansa, Anthony Agbazuere.

Bayan bayyanar bidiyon Agbazuere yana watsa wa Odumeje, 'Indaboski', kudi ya yi ta yawo a kafafen sada zumunta, The Cable ta ruwaito.

A bidiyon an ga Agbazuere yana manna wa Chukwuemeka Ohanaemere wanda aka fi sani da Odumeje, wannan sanannen faston na Onitsha, yana kwasar rawa. Duk da dai ba a san lokacin da aka dauki bidiyon ba, amma ko da gani Agbazuere yana kujerarsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel