Buhari ya magantu a kan nasarar APC a zabukan maye gurbi

Buhari ya magantu a kan nasarar APC a zabukan maye gurbi

- APC ta kara samun tabbaci a kan cewa har yanzu 'yan Najeriya suna yayin jam'iyyar, sakamakon nasarar da suka samu a zaben maye gurbi

- Hadimin shugaban kasa na harkar yada labarai, Mallam Garba Shehu, ya ce Shugaba Buhari yayi farinciki da yadda APC ta samu nasara

- Ya mika sakon godiyarsu ga duk wadanda suka amince da mulkin Buhari, yana mai tabbatar musu cewa ba za su basu kunya ba

Jam'iyyar APC ta kara samun tabbacin cewa har yanzu 'yan Najeriya ita suke yayi, bayan ganin dumbin nasarorin da ta samu a zaben maye gurbi da aka yi, kamar yadda fadar shugaban kasa tace.

Malam Garba Shehu, babban hadimin shugaba Muhammadu Buhari a kan harkar yada labarai ya sanar da hakan.

A wata takarda da ya saki a Abuja ranar Lahadi, 6 ga watan Disamba, kakakin shugaban kasa yace hakika Shugaba Muhammadu Buhari ya yi matukar farinciki da jin nasarorin da APC ta samu a zaben maye gurbin da aka yi.

Buhari ya magantu a kan nasarar APC a zabukan maye gurbi
Buhari ya magantu a kan nasarar APC a zabukan maye gurbi. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: UGC

KU KARANTA: Tirkashi: APC ta lashe kujerar sanatan Imo amma babu takamaiman dan takara

Kamar yadda ya wallafa a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter: "Ba za mu dauki wannan tabbacin da ku ka ba mu a banza ba, kuma ba za mu baku kunya ba.

"Yan Najeriya masu yaba wa da kokarin da wannan mulkin yake yi na ganin an samar wa kowa ingantacciyar rayuwa, musamman yadda tattalin arzikin kasa ya lalace sakamakon annobar Coronavirus, ba za mu ba su kunya ba."

A wata takarda da NAN ta ruwaito, Shehu ya yi godiya ga 'yan Najeriya a kan amincewa da mulkin Buhari.

KU KARANTA: Maryam Sanda: Dalilai 3 da suka sa kotun daukaka kara ta jaddada hukuncin kisa

Ya kara da cewa, "Muna godiya ga kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC, karkashin mulkin Mai Mala Buni, gwamnan jihar Yobe da PGF, karkashin shugabancin gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Bagudu.

"Muna kuma godiya ga gwamnoninmu, shugabannin jam'iyya na kananun hukumomi har zuwa gunduma, saboda jajircewarsu da kokarinsu har aka samu wannan nasarar."

A wani labari na daban, an kashe wasu mutane 2 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a wuraren Sanyinna da ke karamar hukumar Tambuwal a jihar Sokoto, yayin harbe-harbe da 'yan sanda.

Kwamishinan 'yan sanda, Ibrahim Sani Ka'oje ya bayyana hakan a ranar Asabar a wani taro da suka yi a hedkwatar 'yan sanda, Channels TV ta wallafa.

Kamar yadda yayi bayani, ana zargin daya daga cikinsu da fashi da makamai a sati 2 da suka wuce, inda ya kashe mutane 2 a wuraren Tamaje da ke jihar, amma an damke shi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel