Rashin tsaro: Gungun ‘Yan PDP a Majalisa suna neman a sauke Shugaba Buhari

Rashin tsaro: Gungun ‘Yan PDP a Majalisa suna neman a sauke Shugaba Buhari

- ‘Yan PDP a Majalisar Wakilai suna so jama’a su dage a kan a tsige Shugaban kasa

- Kingsley Chinda ya kuma bukaci Majalisar FEC ta yi waje da Muhammadu Buhari

- Bangaren jam’iyyar APC suna ganin babu dalilin a kawo maganar tunbuke Buhari

Bangaren jam’iyyar PDP a majalisar wakilan tarayya ta yi kira ga ‘yan Najeriya su tursasa wakilansu domin a fara yunkurin tsige shugaban kasa.

Shugaban ‘yan majalisar PDP marasa rinjaye a majalisar tarayyar, Honarabul Kingsley Chinda ya bayyana wannan a wani jawabi da ya fitar ranar Lahadi.

Kingsley Chinda mai wakiltar yankin jihar Ribas a karkashin jam’iyyar PDP yake cewa ya kamata a sauke Muhammadu Buhari daga kan karagar mulki.

Daily Trust ta ce a jawabinsa, Hon. Chinda yace shugaban kasar ya na cigaba da saba sashe na 14(2) (b) kundin tsarin mulkin Najeriya dalilin gazawarsa.

KU KARANTA: Mai takaba ta gaje kujerar Marigayin Mai gidanta a PDP

Bangaren jam’iyyar PDP a majalisar suna ao majalisar FEC ta Ministoci suyi amfani da sashe na 144(1) na kundin tsarin mulki, su yi waje da shugaban kasar.

Chinda ya nemi majalisar zartarwa ta Najeriya ta bayyana cewa Buhari ya gaza sauke nauyin da ke kansa na kare rai da kuma dukiyar al’ummar dake kansa.

‘Yan majalisar hamayyar suka ce: “’Yan ta’ddda da ‘yan bindiga su na kashe ‘yan Najeriya kullum babu yadda aka iya, yayin da tattalin arziki yake koka wa.”

‘Yan majalisar sun yi tir da hari da satar mutane da ake yi a irinsu Buni Yadi, Gamboru, Baga, Gwoza, Shiroro, Konduga, Kawuri, Kaduna, da yankin Benuwai.

KU KARANTA: Bawan Allah ya yi kicibis da wanda ya yi garkuwa da shi a mota

Rashin tsaro: Gungun ‘Yan PDP a Majalisa suna neman a sauke Shugaba Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Shugaban masu rinjaye a majalisa, Hon. Ado Alhassan Doguwa, ya maida martani, yace a wannan lokaci shirmen banza ne a rika maganar tsige shugaban kasa.

A jiya mun tuna maku da lokacin da Mai girma Muhammadu Buhari ya zargi Gwamnatin Goodluck Jonathan da hannu a rikicin Boko Haram da ake yi.

Mun bankado wata tsohuwar hirar da Buhari ya yi da ‘Yan jarida ne kan Boko Haram shekaru 9 da suka wuce, a wancan lokaci bai zama shugaban kasa ba tukuna.

Buhari ya caccaki gwamnatin Najeriya a wancan lokaci, ya ce ita ce babbar Boko Haram a kasar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel