Tuna baya: Abin da Muhammadu Buhari ya fada game da Boko Haram a 2011

Tuna baya: Abin da Muhammadu Buhari ya fada game da Boko Haram a 2011

- A wata hira da aka yi a 2011, Muhammadu Buhari ya zargi gwamnati da hannu a rikicin Boko Haram

- Bayan shekaru kadan da yin wannan magana, Buhari ya samu mulkin kasar, amma har yau ana ta fama

Mun lalubo wani tsohon faifan sauti da aka yi hira da Muhammadu Buhari a shekarar 2011, inda ya fito yana zargin gwamnati da hannu a rikicin Boko Haram.

Janar Muhammadu Buhari ya yi wannan jawabi ne a lokacin da aka yi hira da shi a VOA Hausa. Sai bayan shekaru hudu da yin wannan magana, ya hau mulki.

Da ake maganar rikicin, sai ya ce:

“Wannan nauyi na daura shi ne a kan gwamnatin tarayya, saboda su wanene suke da ‘yan sanda, su wa suke da sojojin kasa da na sama da na ruwa?"

Ya aka yi aka fara ta’addancin Kudu maso kudu, wadanda har yau suna bala’i. Har yau na ji ana fadin an kashe ‘yan sanda 11 ko 12, wanda aka kona su, aka kashe.

KU KARANTA: Ana sauraron Buhari a zauren Majalisa saboda halin rashin tsaro

Buhari ya sake zargin gwamnati, yace: “Su wanene su kayi sanadin fara Boko Haram, idan gwamnatin tarayya da gaske take yi, za a iya maganin wannan abu.

Yake cewa: “Ko kuwa sai dai a zauna har su (‘Yan ta’addan Boko Haram) su rushe Najeriya."

Shugaban na Najeriya a yau, yace yana goyon bayan yi wa ‘yan ta’addan Boko Haram afuwa. “Za tayi amfani mana, idan an san su wanene shugabanninsu.”

Buhari ya ce irin wannan afuwa tayi tasiri a kan tsagerun Neja-Delta dake tada kafar-baya, wanda bayan an yi masu afuwa, an samu saukin ta’adi a yankin Kudu.

“Su ma wadannan idan sun fito an sansu, ayi magana da su.”

Tuna baya: Abin da Muhammadu Buhari ya fada game da Boko Haram a 2011
Muhammadu Buhari Hoto:www.channelstv.com
Asali: UGC

KU KARANTA: An kashe masu garkuwa da mutane a Sokoto

A jawabinsa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa Boko Haram guda uku ce: da ta Muhammadu Yusufu, da barayi (daga jami’an tsaro) da kuma gwamnatin PDP.

“Ita kuma gwamnatin tarayyar da ‘yan ta’addanta, ta kashe mutane, gwamnati tace ba su bane.” Ya karkare da cewa: “Halin da muke ciki kenan…kuma kowa ya sani.”

A ranar Lahadin nan kun ji cewa Ministan sufuri na kasa, Rotimi Chibuike Amaechi ya nuna ya na shirin dawowa da karfinsa domin karbe jihar Ribas a 2021.

Tsohon gwamnan wanda ya bar PDP ya shiga APC a 2014, ya bugi kirjin cewa idan ya dawo, zai murza kambu domin duk abunda ya fadi haka zai kasance haka.

A cewar Amaechi, ba ya kabilanci wanda hakan ne dalilin da yasa yayi aiki domin ganin nasarar Muhammadu Buhari a 2015, a maimakon Goodluck Jonathan.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel