Direba ya gane wanda ya taɓa garkuwa da shi cikin fasinjojin da suka shiga motarsa a Sokoto

Direba ya gane wanda ya taɓa garkuwa da shi cikin fasinjojin da suka shiga motarsa a Sokoto

- Direba ya gane wanda ya taba garkuwa da shi daga cikin fasinjojin sa a tashar Kwannawa da ke jihar Sokoto

- Direban wanda aka yi garkuwa da shi watanni biyu da suka gabata a Kankara da ke jihar Katsina ya yi saurin gane mutumin kuma ya sanarwa da shugabbanin tashar

- Yan sanda sun kama wanda ake zargin kuma tuni aka maida al'amarin zuwa hedikwatar yan sanda ta Sokoto don fadada bincike

Wata dambarwa ta faru a tashar mota ta Kwannawa da ke Karamar Hukumar Dange-Shuni a jihar Sokoto bayan da wani direba ya shaida wanda ya yi garkuwa da shi a cikin fasinjojinsa.

Direban wanda ba'a bayyana sunan shi ba, an yi garkuwa da shi a Kankara da ke jihar Katsina watanni biyu da suka gabata.

Direba ya gane wanda ya taba garkuwa da shi cikin fasinjojinsa
Direba ya gane wanda ya taba garkuwa da shi cikin fasinjojinsa. Hoto: @daily_trust
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa direban ya shafe kimanin sati uku a tsare bayan biyan kudin fansar da ba'a bayyana adadin su ba.

DUBA WANNAN: Hisbah ta yi bincike ɗaki-ɗaki don kama masu baɗala a Kano (Hotuna)

Wanda ake zargin ya gamu da cikas, lokacin da ya shiga mota zuwa Kano, ba tare da sanin ita ce motar da suka tare suka yi garkuwa da direba ba.

"Direban ya yi saurin gane shi saboda abin bai dade da faruwa ba.

"Bayan gane shi, ya yi gaggawar sanar da Shugabannin kungiya su kuma suka sanar da yan sanda mafi kusa," wani dan kungiyar direbobi NURTW ya shaidawa manema labarai.

Shugabannin Kungiyar sun chanja direban motar da wani bayan motar ta cika da fasinja kuma ya nufi garin Shuni.

An ruwaito cewa a nan yan sanda suka kama wanda ake zargin zuwa ofishin su.

KU KARANTA: Mutum 20 sun mutu, 14 sun jikkata a hatsarin mota a Sokoto

Da ake tuhumar sa, ya bayyana cewa shi dan kungiyar masu garkuwa da mutane ne kuma ana kiran sa 'Hadari' kuma aka hada shi da direban don amsa tambaya.

"Yan sanda sun yi mamakin yadda yadda direba ya fadi sunan duk da baya nan lokacin da ake tuhumar," a cewar majiyar mu.

An mayar da wanda ake zargin zuwa hedikwatar yan sanda ta jihar Sokoto don fadada bincike.

Mai magana da yawun rundunar, DSP Muhammad Sadiq ya tabbatar da faruwar lamarin, kuma ya ce bincike su ke har yanzu.

A wani labarin, tsohon shugaban majalisar dattawar Najeriya, Sanata Joseph Wayas, yana wata asibiti a birnin Landan sakamakon rashin lafiya da ya ke fama da ita kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Sanata Wayas shine shugaban majalisar dattawa a jamhuriya ta biyu daga shekarar 1979 zuwa 1983 a lokacin da marigayi Alhaji Shehu Shagari ke shugaban kasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel