Zaben cike gurbi na Cross River: Yar takarar PDP Akwaji ta lallasa na APC
- An kaddamar da PDP a matsayin wacce ta lashe zaben cike gurbi na mazabar Obudu a Cross River
- INEC ta sanar da Maria Godwin Akwaji ta PDP a matsayin wacce ta lashe zaben a ranar Lahadi, 6 ga watan Disamba
- Akwaji ta samu kuri’u 32,166, yayinda abokin adawarta, Abor Adaje Godwin na APC ya samu kuri’u 3,546
- Maria ta gaji mijinta, Akwaji (dan majalisa), wanda ya mutu a watan Yuni bayan dan jinya
Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) a ranar Lahadi, 6 ga watan Disamba, ta kaddamar da jam’yyar Peoples Democratic Party (PDP) a matsayin wacce ta lashe zaben cike gurbi na Cross River a mazabar Obudu.
Yar takarar PDP, Maria Godwin Akwaji, ta lallasa abokin hamayyarta na All Progressives Congress (APC), Abor Adaje Godwin.
Baturen zabe na INEC, Farfesa Abel Ezeoha, ya sanar a ranar Lahadi cewa yayinda Akwaji ta samu kuri’u 32, 166, Godwin ya samu kuri’u 3, 546 ne kawai, Channels TV ta ruwaito.
KU KARANTA KUMA: Ba na nuna kabilanci: Amaechi ya magantu a kan barin Jonathan da goyawa Buhari baya
Maria ta kasance matar marigayi Akwaji, dan majalisa a jihar wanda ya mutu a watan Yunin 2020 sakamakon cutar corona.
A gefe guda, hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta kaddamar da dan takarar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben cike gurbi na sanata mai wakiltan Cross River ta arewa.
An dai gudanar da zaben cike gurbin ne a ranar Asabar, 5 ga watan Disamba.
KU KARANTA KUMA: Ndume da sauran Sanatoci 5 da muryarsu ta fi amo a shekarar 2020
Baturen zaben cike gurbin, Farfesa Ameh Akoh na jami’ar tarayya ta Alex Ekwueme, Ikwo, jihar Ebonyi, shine ya sanar da sakamakon zaben, jaridar Vanguard ta ruwaito.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.n
Asali: Legit.ng