'Yan sanda sun kashe masu garkuwa da mutane 2, sun cafke 'yan fashi a Sokoto
- An kashe wasu mutane 2 da ake zargin 'yan fashi ne a karamar hukumar Tambuwal dake jihar Sokoto
- Sannan 'yan sandan sun samu nasarar damkar wasu masu garkuwa da mutane guda 8
- An samu bindigogi kirar AK-47 a hannunsu, da kuma sauran miyagun makamai
An kashe wasu mutane 2 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a wuraren Sanyinna da ke karamar hukumar Tambuwal a jihar Sokoto, yayin harbe-harbe da 'yan sanda.
Kwamishinan 'yan sanda, Ibrahim Sani Ka'oje ya bayyana hakan a ranar Asabar a wani taro da suka yi a hedkwatar 'yan sanda, Channels TV ta wallafa.
Kamar yadda yayi bayani, ana zargin daya daga cikinsu da fashi da makamai a sati 2 da suka wuce, inda ya kashe mutane 2 a wuraren Tamaje da ke jihar, amma an damke shi.
Fashi 4 da aka yi, wanda aka kama mutane 8 da ake zargin 'yan fashi ne da miyagun makamai. Garin hakan ne aka amshi AK-47 da sauran miyagun makamai daga hannunsu.
KU KARANTA: 2023: Jigo a APC ya bayyana mutanen da za su fitar da yankin shugaban kasa
KU KARANTA: Bidiyon soja yana dukan budurwa tare da yi mata tsirara a titi kan shigar banza
A wani labari na daban, wata yarinya ta koma sana'ar tukin keke-Napep don kulawa da kanninta da kuma biyan basukan da ake bin mahaifnta da ya mutu.
Wata Kaothar Ajani, mai shekaru 16, ta zage wurin sana'ar tukin Keke-Napep bayan mutuwar mahaifinta. Tana sana'ar ne don kulawa da kanta da mahaifiyarta.
A al'adar Afirika, akwai ayyuka daban-daban wadanda aka saba maza ne suke yi, ba haramun ne mata su yi ba, amma kuma maza ne suka yi fice a sana'o'in.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng