Majalisa: Watakila mu ga zuwan Shugaban kasa a ranar 10 ko 15 ga watan nan

Majalisa: Watakila mu ga zuwan Shugaban kasa a ranar 10 ko 15 ga watan nan

-‘Yan Majalisar Wakilai sunyi karin haske game da hallarar Shugaban kasa

-Ana sa ran Muhammadu Buhari ya bayyana gaban Majalisa a ranar Alhamis

-Taron APC ne ya sa Shugaban kasa ba zai bayyana tun a ranar 8 ga wata ba

A dalilin kashe-kashen da ake ta yi a Najeriya wanda sun ki ci, sun ki cinye wa, shugaba Muhammadu Buhari zai bayyana gaban majalisa.

Shugaban kasar ya amince zai hallara a zauren majalisar tarayya domin yi masu karin bayani game da abin da ke faru wa, da irin kokarin da yake yi.

Mai magana da yawun bakin ‘yan majalisar wakilan tarayya, Honarabul Benjamin Kalu, ya yi karin-haske game da bayyanar shugaban Najeriyar.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta bayyana, Benjamin Kalu ya ce za a iya ganin Muhammadu Buhari a ranar Alhamis 10 ga watan Disamban 2020.

KU KARANTA: Karya ce ace duk Duniya babu masu karbar albashi irin Majalisar Najeriya

Idan kuma shugaban kasar bai zo majalisa a wannan rana ba, za a saurari zuwan sa a ranar Talata, 15 ga watan Disamba, 2020, a cewar Benjamin Kalu.

‘Dan majalisar ya bayyana wannan ne jiya a lokacin da ya hadu da manema labarai a garin Abuja.

Da ya ke magana da ‘yan jarida a ranar 3 ga watan Disamba, Kalu ya ce taron jam’iyyar APC da za ayi a makon gobe, ba zai ba Buhari damar zuwa kafin nan ba.

Idan za ku tuna majalisar koli watau NEC ta APC ta kira taro a ranar 8 ga watan Disamba, shugaban kasa da sauraron jagororin jam’iyya duk zasu halarta.

KU KARANTA: Kisan manoma a Zabarmari ya ci ace an sauke Hafsun Sojoji - NAS

Majalisa: Watakila mu ga zuwan Shugaban kasa a ranar 10 ko 15 ga watan nan
Majalisar Wakilai Hoto: Twitter/@HouseNgr
Asali: Twitter

Hon. Kalu ya ce: "Saboda haka, muna sa ran ranar 10 ko 15 ga watan Disamba, Shugaban kasa ya riga ya karya lagon nan, ya ce zai bayyana a gaban majalisa.”

A zaman da aka yi a tsakiyar makon nan a majalisa, kun ji cewa Sanata Kashim Shettima ya ce sun fuskanci hare-hare fiye da 2000 a cikin wannan shekara.

Tsohon Gwamnan na Jihar Borno ya jero ta’adin Boko Haram a 2020, yace sau 2801 'yan ta'addan Boko Haram su na kawo masu hari daga Junairu zuwa yanzu.

Kashim Shettima ya fada wa Shugaba Buhari cewa ya sani Hafsun Sojin kasar duk sun gaza.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel