Dan takarar APC Kurami ya lashe zaben cike gurbi a Katsina

Dan takarar APC Kurami ya lashe zaben cike gurbi a Katsina

- Hukumar zabe ta bayyana dan takarar APC a matsayin wanda ya lashe zaben cike gurbi na mazabar Bakori ta jihar Katsina

- Dr. Ibrahim Aminu Kurami na APC ya samu kuri'u 20,444, babban abokin hamayyarsa na PDP, Alhaji Aminu Magaji kuma ya samu kuri’u 11,356

- An dai yi zaben ne a ranar Asabar, 5 ga watan Disamba sannan aka sanar da sakamako a yau Lahadi

An kaddamar da Dr. Ibrahim Aminu Kurami na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a matsayin wanda ya lashe zaben cike gurbi na mazabar Bakori ta jihar Katsina a yau Lahadi, 6 ga watan Disamba.

An gudanar da zaben ne a ranar Asabar, 5 ga watan Disamba.

Kurami ya kayar da Alhaji Aminu Magaji na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), jaridar The Nation ta ruwaito.

Dan takarar APC Kurami ya lashe zaben cike gurbi a Katsina
Dan takarar APC Kurami ya lashe zaben cike gurbi a Katsina Hoto: @vanguardngrnews
Source: Twitter

Da yake sanar da sakamakon karshe, baturen zaben cike gurbi na karamar hukumar Bakori, Farfesa A. D. kankia, ya kaddamar da cewa Dr. Aminu Kurami na APC ya samu kuri’u 20,444.

Sannan shi kuma babban abokin hamayyarsa, Alhaji Aminu Magaji na PDP ya samu kuri’u 11,356.

KU KARANTA KUMA: Zaben cike gurbi na Cross River: Yar takarar PDP Akwaji ta lallasa na APC

Legit.ng ta tuna cewa mamba mai wakiltan mazabar Bakori a majalisar dokokin jihar, Alhaji Abdulrrazaq Tsiga ya mutu a watan Mayun wannan shekarar bayan rashin lafiya.

Tsiga ya kamu da rashin lafiya ne Jim kadan bayan rantsar da shi a majalisar dokokin Katsina a watan Yunin 2019.

Ya kasance mataimakin shugaban masu rinjaye a majalisar kuma shugaban kwamitin majalisar kan kasuwanci, da’a da damammaki kafin mutuwarsa.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: INEC ta kaddamar da PDP a matsayin wacce ta lashe zaben cike gurbi na Sanata a Cross River ta arewa

A gefe guda, an sanar da yar takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben cike gurbin kujerar sanata na Plateau ta kudu, Farfesa Nora Dabu’ut a matsayin wacce ta yi nasara.

A bisa ga sakamakon da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta sanar, Farfesa Idris A Male, shugaban jami’ar tarayya ta Lafia, jihar Nasarawa, a Shendam, ya ce Dubu’ut ta samu kuri’u 83,151.

Sannan abokin hamayyarsa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Georgia Daika ya samu kuri’u 70,838.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel