Yanzu Yanzu: Zaben cike gurbi: APC ta lashe kujerar Sanata a Plateau ta kudu

Yanzu Yanzu: Zaben cike gurbi: APC ta lashe kujerar Sanata a Plateau ta kudu

- Yar takarar jam'iyyar APC a zaben cike gurbin kujerar sanata na Plateau ta kudu, Farfesa Nora Dabu’ut ta lashe zaben

- Hakan na kunshe ne a cikin takardar sanar da sakamako da hukumar INEC ta fitar a ranar Lahadi, 6 ga watan Disamba

- Yar takarar ta APC ta kawo kananan hukumomi hudu cikin shida inda shi kuma na PDP ya kawo sauran biyun

An sanar da yar takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben cike gurbin kujerar sanata na Plateau ta kudu, Farfesa Nora Dabu’ut a matsayin wacce ta yi nasara.

A bisa ga sakamakon da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta sanar, Farfesa Idris A Male, shugaban jami’ar tarayya ta Lafia, jihar Nasarawa, a Shendam, ya ce Dubu’ut ta samu kuri’u 83,151.

Sannan abokin hamayyarsa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Georgia Daika ya samu kuri’u 70,838.

Yanzu Yanzu: Zaben cike gurbi: APC ta lashe kujerar Sanata a Plateau ta kudu
Yanzu Yanzu: Zaben cike gurbi: APC ta lashe kujerar Sanata a Plateau ta kudu Hoto: Fresh reporters
Source: UGC

Farfesa Dabu’ut ta kayar da abokin hamayyarta a kananan hukumomi hudu cikin shida da ke yankin, jaridar The Nation ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: INEC ta kaddamar da PDP a matsayin wacce ta lashe zaben cike gurbi na Sanata a Cross River ta arewa

Shi kuma Daika ya kawo sauran kananan hukumomi biyu da suka rage.

Ga sakamakon zaben dukkanin kananan hukumomin a kasa:

Karamar hukumar Langtang ta arewa

APC: 12241

PDP: 16841

Banbancin kuri'u: 4,600

Karamar hukumar Langtang ta kudu

APC: 9321

PDP: 12439

Banbancin kuri'u: 3,118

Karamar hukumar Mikang

APC: 8425

PDP: 7887

Banbancin kuri'u: 538

Karamar hukumar Shendam

APC: 18542

PDP: 10223.

Banbancin kuri'u: 8,319.

Karamar hukumar Qyan-pan

APC: 12,784

PDP: 10, 641.

Banbancin kuri'u: 2,143

Karamar hukumar Wase

APC: 21,838

PDP: 12,807

Banbancin kuri'u: 9,031

KU KARANTA KUMA: Ba na nuna kabilanci: Amaechi ya magantu a kan barin Jonathan da goyawa Buhari baya

A wani labarin, hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) a ranar Lahadi, 6 ga watan Disamba, ta kaddamar da jam’yyar Peoples Democratic Party (PDP) a matsayin wacce ta lashe zaben cike gurbi na Cross River a mazabar Obudu.

Yar takarar PDP, Maria Godwin Akwaji, ta lallasa abokin hamayyarta na All Progressives Congress (APC), Abor Adaje Godwin.

Baturen zabe na INEC, Farfesa Abel Ezeoha, ya sanar a ranar Lahadi cewa yayinda Akwaji ta samu kuri’u 32, 166, Godwin ya samu kuri’u 3, 546 ne kawai, Channels TV ta ruwaito.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel