Yanzu Yanzu: INEC ta kaddamar da PDP a matsayin wacce ta lashe zaben cike gurbi na Sanata a Cross River ta arewa

Yanzu Yanzu: INEC ta kaddamar da PDP a matsayin wacce ta lashe zaben cike gurbi na Sanata a Cross River ta arewa

- Hukumar INEC ta kaddamar da dan takarar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben cike gurbi na Sanata a Cross River ta arewa

- Baturen zaben, Farfesa Ameh Akoh ne ya sanar da hakan a yau Lahadi, 6 ga watan Disamba

- Dr Stephen Odey ya samu kuri’u 129,207 wajen kayar da sauran yan takara takwas da suka fafata da shi

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) a ranar Lahadi, 6 ga watan Disamba, ta kaddamar da dan takarar jam’iyyar of People’s Democratic Party (PDP), Dr Stephen Odey, a matsayin wanda ya lashe zaben cike gurbi na sanata mai wakiltan Cross River ta arewa.

An dai gudanar da zaben cike gurbin ne a ranar Asabar, 5 ga watan Disamba.

Baturen zaben cike gurbin, Farfesa Ameh Akoh na jami’ar tarayya ta Alex Ekwueme, Ikwo, jihar Ebonyi, shine ya sanar da sakamakon zaben, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Yanzu Yanzu: INEC ta kaddamar da PDP a matsayin wacce ta lashe zaben cike gurbi na Sanata a Ribas ta arewa
Yanzu Yanzu: INEC ta kaddamar da PDP a matsayin wacce ta lashe zaben cike gurbi na Sanata a Ribas ta arewa Hoto: @vanguardngrnews
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Ndume da sauran Sanatoci 5 da muryarsu ta fi amo a shekarar 2020

Ya ce dan takarar PDP, Dr Stephen Odey ya samu kuri’u 129,207 wajen kayar da sauran yan takara takwas.

A cewarsa, dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress, APC, Mista Joe Again (SAN) ya samu kuri’u 19,165 wajen zama na biyu.

Sannan kuma dan takarar African Democratic Congress, Mista Gregory Agam ya zo na uku da kuri’u 388.

“An kaddamar da dan takarar PDP a matsayin wanda ya lashe zabe daidai da gudanarwar zaben bayan ya samu kuri’u mafi yawa,” in ji shi.

Hakazalika, Misis Maria Akwaji ta lashe zabe a zaben cike gurbi na mazabar Obudu ta jiha bayan ta samu kuri’u 32,166 wajen kayar da abokin hamayyarta, Mista Abor Adaji na APC wanda ya samu kuri’u 3,546.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya aika wakilci mai karfi zuwa daurin auren diyar hadiminsa a Kano

A wani labarin, ministan sufuri, Chuibuke Amaechi, ya ce ya zabi kasancewa da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2015 maimakon Gooduck Jonathan saboda shi baya nuna kabilanci.

Tsohon gwamnan na jihar Ribas ya yi ikirarin cewa Jonathan ya gabatar masa da kawara daban-daban don ya ci gaba da kasancewa a jam’iyyar PDP, amma ya ki amsa tayinsa.

Ya ce a lokacin da ya bar jam’iyyar, tsohon Shugaban kasar yayi fada da shi amma ya yi nasarar shawo kan lamarin saboda Allah na tare da shi.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel