An cafke wanda ya tare Sanata Abbo, ya ce sai an biya Miliyan 2 inji Hadiminsa

An cafke wanda ya tare Sanata Abbo, ya ce sai an biya Miliyan 2 inji Hadiminsa

- Sanata Ishaku Elisha Abbo ya shawo kan wani da ya taso masa da bindiga

- ‘Dan Majalisar ya ci karo da wannan mutum ya na hanyar zuwa bikin aure

- Jawabin da aka fitar daga ofishin Sanatan yace har an cafke wannan tsagera

Rahotanni sun shaida mana cewa Sanata mai wakiltar yankin Adamawa ta Arewa a majalisar dattawa, Ishaku Elisha Abbo ya tsallake rijiya da baya.

Labarin da Legit.ng ta samu daga ofishin yada labarin ‘dan majalisar shi ne ya fafata da wani mutumi da ya auka masa dauke da ‘yar karamar bindiga.

Wannan mutum yayi barazanar harbe ‘dan majalisar idan ba a ba shi kudi har Naira miliyan biyu ba.

KU KARANTA: Wanene Sanata Elisha Abbo?

Hadimin Sanatan, Michael Volgent, shi ne ya fitar da jawabi a madadinsa, yace wannan mummunan abu ya faru ne da kimanin karfe 2:00 na tsakar dare.

Sanata Ishaku Elisha Abbo ya na hanyarsa na zuwa bikin dauren wani auren wani daga cikin ‘yanuwansa ne a garin Mubi a lokacin da abin ya faru.

Michael Volgent yace an yi yunkurin ganin bayan matashin ‘dan siyasar ne a wannan hari.

Mista Volgent ya fitar da wannan jawabi yana mai karyata rade-radin dake yawo daga wani bidiyo na cewa mai gidansa mutum ne mai saurin hannu.

KU KARANTA: Abbo ya samu sabani da Gwamna Fintiri a PDP

An cafke wanda ya tare Sanata Abbo, ya ce sai an biya Miliyan 2 inji Hadiminsa
Elisha Abbo Hoto: www.bbc.com/hausa
Source: UGC

Kamar yadda jawabin da Michael Volgent ya yi ya bayyana, jami’an tsaro sun yi gaba da wannan mutumi wanda ya yi wa Sanatan barazana da makami.

Abbo ya ce rashin aikin yi da talauci suke jawo irin wannan miyagun halaye a al’umma, ya sha alwashin cigaba da ba jama'a tallafi a gobe ranar Asabar.

A watan Nuwamba ne Sanata Ishaku Abbo ya canza shekar siyasa, Sanatan ya canza jam'iyyarsata PDP zuwa APC mai mulki dake da rinjaye a majalisar tarayya.

A cewarsa 'dan majalisar, da a cikin duhu yake, sai yanzu ya koma cikin haske da ya koma APC.

Abbo ya ce ya koma jam'iyyar APC ne saboda jam'iyya ce da take tafiya a kan adalci. Kafin ya bar PDP, Matashin ya yi ta sukar gwamnansa Amadu Fintiri.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel