Rikici ya barke tsakanin gwamnan Adamawa da Sanata Elisha Abbo

Rikici ya barke tsakanin gwamnan Adamawa da Sanata Elisha Abbo

Rikici ya barke tsakanin Sanata Elisha Abbi da gwamnan jihar Adamawa, Umaru Fintiri, kan zaben kananan hukumomin jihar inda aka hana wasu takara karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP.

Sanata Abbo ya tuhumci gwamnan da laifin takewa wasu mambobin jama'ar hakki kuma ya ce ba'a mayar da hankali ba, Fintiri zai kashe PDP a jihar.

Daily Nigerian ta bada rahoton cewa Sanata Abbo ya laburta hakan ne a jawabin da ya saki a shafin ra'ayi da sada zumuntarsa ta Facebook ranar Litinin.

A cewarsa, girman kan Fintiri zai kai jam'iyyar PDP ya baro muddin bai daina wadannan halaye ba.

Sanatan ya ce kwamitin tantance yan takara ta hana magoya bayansa takara a zaben karkasin jagorancin wani aminin gwamnan, Kwamoti La'ori.

KU KARANTA: Ku yi hakuri - Shugaban kasar Afirka ta kudu ya nemi afuwan yan Najeriya

Yace: "Ya kamata in bayyana wannan saboda tarihi, na gana da gwamnan sau uku gaban jama'a kan wannan zaben kananan hukumomi da za'a gudanar kuma ya tabbatar mana da cewa ba zai sa baki ba, ashe karya yake yi."

"Ya bada umurnin soke yan takaran da ke kusa da ni bayan gane cewa yan takaransa ba zasu samu nasara ba."

"Ya kamata jama'a su sani cewa, gwamna Fintiri ya yi iyakan kokarinsa wajen ganin cewa na fadi a zaben fidda gwani. Har kwanan yayi a Mubi inda yake shirya kaidin kayar da ni,"

Sanata Abbi ya yi kira ga uwar jam'iyyar ta dauki mataki kafin miyan tayi tsami.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel