Lai Mohammed ya ce sai Buhari ya kammala wa’adinsa duk da kira da ake yi na yayi murabus

Lai Mohammed ya ce sai Buhari ya kammala wa’adinsa duk da kira da ake yi na yayi murabus

- Daga karshe gwamnatin tarayya ta yi martani a kan kira ga murabus din shugaba Buhari

- Ministan labarai da al’adu, Lai Mohammed ya yi bayani kan dalilin da yasa Shugaban kasar ba zai yi murabus ba

- Mohammed ya dasa ayar tambaya kan kudirin masu kira ga Buhari ya sauka daga mulki

Ministan labarai da al’adu, Lai Mohammed ya bayyana cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kammala wa’adin mulkinsa duk da kiraye-kiraye da ake yi na yayi murabus.

Da yake magana a wajen wani ganawa da kungiyar mamallakan jaridun Najeriya (NPAN) a Lagas a ranar Alhamis, 3 ga watan Disamba, Mohammed ya ce kira da ake na Shugaban kasar yayi murabus siyasa ce.

A cewar jaridar Punch, ya bayyana bukatar Shugaban kasa yayi murabus kafin kammala wa’adin mulkinsa saboda kisan wasu manoma a jihar Borno a matsayin rashin tunani.

Lai Mohammed ya ce sai Buhari ya kammala wa’adinsa duk da kira da ake yi na yayi murabus
Lai Mohammed ya ce sai Buhari ya kammala wa’adinsa duk da kira da ake yi na yayi murabus Hoto: @MBuhari
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Hotunan kamun auren jarumin Kannywood, Nuhu Abdullahi

Mohammed yace:

“A tsaka da lamarin kashe-kashe, ana ta kira a wasu bangarori kan Shugaban kasar yayi murabus.

“Don haka, bari na fadi cewa wannan kira shiri ne na buga kazamar siyasa da lamarin tsaro, kuma hakan rashin tunani ne. An zabi Shugaban kasar a 2015 na tsawon shekaru hudu sannan aka sake zabarsa a 2019 don ya sake wasu shekaru hudun.”

Ya jaddada cewa babu yawan kira da za a yi masa na yayi murabus da zai hana Shugaban kasar cike wa’adinsa.

Ministan ya ce kokarin janye hankali da kazamar siyasa ce ke sa ake neman Shugaban kasar ya sauka daga mulki a duk lokacin da aka samu akasi a yaki da ta’addanci.

KU KARANTA KUMA: DHQ ta maida martani ga NGF, ta ce yakin Boko Haram bai fi karfinta ba

A baya mun ji cewa, kungiyar dattawan arewa ta sake sabonta kiran da take yi na neman Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi murabus.

Da yake magana a yayin hira da Channels Television a ranar Laraba, 2 ga watan Disamba, kakakin kungiyar, Hakeem Baba-Ahmed, ya ce hujjojin da ke kasa sun marawa kiraye-kiraye da suke yi ga Shugaban kasar yayi murabus a baya.

Ya ce: “Hujjar da ke kasa ya marawa abunda muke fadi baya. Shugaban kasar ya yi rantsuwa da Al-Qur’ani don kare al’umman kasar. Ya gaza yin hakan.

“Wannan shine shekararsa ta biyar a kan mulki. Halin da ake ciki yana kara tabarbarewa a karkashinsa kuma babu alama da ke nuna abubuwa za su inganta.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng