Akande da Tinubu sun shiga cikin rigimar Aregbesola da Oyetola domin a samu mafita

Akande da Tinubu sun shiga cikin rigimar Aregbesola da Oyetola domin a samu mafita

-Jagororin jam’iyyar APC sun tsoma bakinsu game da rikicin da ake yi a jihar Osun

-APC ta samu kanta a matsala a dalilin sabanin Rauf Aregbesola da Gboyega Oyetola

-Gwamna Adegboyega Oyetola ya samu matsala da tsohon Mai gidansa, Aregbesola

Jagoran APC a kasar Yarbawa, Bola Ahmed Tinubu da wasu kusoshin APC sun kawo karshen rikicin cikin gidan da su ke fama da shi a jihar Osun.

Tsohon gwamnan Legas, Bola Ahmed Tinubu da tsohon gwamnan jihar Osun, Bisi Akande, sun yi wata gana wa da jiga-jigan APC mai mulki a Osun.

This Day ta ce Bisi Akande da Bola Ahmed Tinubu sun sa labule ne da gwamna mai-ci Adegboyega Oyetola da mai gidansa, Rauf Aregbesola.

Bisa dukkan alamu abubuwa ba su tafiya daidai tsakanin Ministan harkokin cikin-gida, Ogbeni Rauf Aregbesola da kuma gwamna Adegboyega Oyetola.

KU KARANTA: Ministan Buhari ya ce FEC ta amince da ayyukan N117b

Wannan ya sa Cif Bisi Akande da Bola Ahmed Tinubu suka kira zama a gidan shi Bisi Akande dake Ila Orangun, inda su kayi wa Minista da gwamnan sulhu.

Mai girma Adegboyega Oyetola shi ne shugaban ma’aikatan fadar Rauf Aregbesola a lokacin da yake gwamna, amma yanzu sun samu matsala a siyasa.

Aregbesola ya samu sabani da magajinsa ne a makon da ya wuce, bayan yaransa sun fara shirya wani biki da sunan murnar nasarorin da aka samu a jihar.

Daga baya dole magoya-bayan Ministan suka hakura da wannan biki da su ka shirya, wanda zai ci karo da ranar da gwamna yake cika shekaru biyu a mulki.

KU KARANTA: Yadda za a samu zaman lafiya a Najeriya - Tinubu

Akande da Tinubu sun shiga cikin rigimar Aregbesola da Oyetola domin a samu mafita
Aregbesola da Gwamna Oyetola Hoto: www.thisdaylive.com
Source: UGC

Duk da haka Ministan ya shigo jihar domin wani aiki na dabam. A nan Tinubu da Akande suka samu damar zama da shi domin sasanta shi da gwamnansa.

A makon da ya gabata kun ji cewa gumurzun siyasa tsakanin jigon jam'iyyar PDP, Bode George, da abokin karawarsa na jam'iyyar APC, Bola Tinubu,ya canza salo.

George ya sake kunno wutar rikici ne bayan ya yi iƙirarin cewar ziyarar da jiga-jigan dattawan jam'iyyar APC suka kai Aso Villa sun yi ne a madadin Bola Tinubu.

A wannan karo ma Tinubu bai maida martani a kan iƙirarin ba, amma wasu sun taya shi fadan.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel