Bola Tinubu ya bada shawarar yadda za a kawo karshen ta'addanci a kasar nan

Bola Tinubu ya bada shawarar yadda za a kawo karshen ta'addanci a kasar nan

- Shugaban jam'iyyarAPC, Bola Tinubu ya ce wajibi ne a hada karfi da karfe idan ana son kawo karshen rashin tsaro a Najeriya

- Tinubu ya bayyana irin kidimewa da gigicewar da yayi bayan jin labarin yadda 'yan Boko Haram suka yi wa manoman Borno kisan wulakanci

- Ya kuma mika sakon ta'aziyyarsa ga gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, da daukacin al'umar jihar a kan kisan manoma 43 na Zabarmari

Shugaban jam'iyyar APC na Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ce sai an zage damtse kafin a samu nasarar yaki da 'yan ta'adda a Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.

A jiya ne Tinubu ya nuna matsananciyar damuwarsa a kan yadda 'yan Boko Haram suka yi wa manoma 43 na jihar Borno kisan wulakanci.

Manoman da basu ji ba basu gani ba, sun mayar da hankulansu wurin nema wa iyalansu abinci, amma rashin tsaro ya janyo musu bala'i.

Bola Tinubu ya bada shawarar yadda za a kawo karshen ta'addanci a kasar nan
Bola Tinubu ya bada shawarar yadda za a kawo karshen ta'addanci a kasar nan. Hoto daga @daily_trust
Source: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: Buhari ya amince bayyana gaban 'yan majalisa a kan rashin tsaro, Gbajabiamila

Ya mika sakon ta'aziyyarsa ga Gwamna Babagana Zulum da daukacin jama'ar jihar Borno a kan kisan monoman kauyen Zabarmari da ke karamar hukumar Jere a jihar.

Ya sanar da hakan ne a wata takarda wacce ya aika wa gwamnan kuma ofishin harkokin yada labaran Tinubu suka bayyana wa manema labarai.

KU KARANTA: Okorocha ga Buhari: Ka fatattaki dukkan masu mukami da hadimanka, sun gaza

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Nasarawa ya rada wa tagwayensa sunan Shugaba Muhammadu Buhari da na Sanata Umar Tanko Al-Makura, jaridar Daily Trust ta wallafa.

Bayan amaryar gwamnan, Hajiya Farida Abdullahi Sule, ta haifi zankada-zankadan ragwayenta, an yi shagalin sunan a ranar Talata a cikin fadar sarkin Gudu a karamar hukumar Akwanga, Alhaji Sule Bawa, wanda shine mahaifin gwamnan.

Gwamnan ya ce: "Na radawa yarana sunayen shugaba Muhammadu Buhari da na Sanata Umar Tanko Al-Makura saboda girmamawa ta a garesu."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel