Jam'iyyar APC ta shirya taron NEC na gaggawa, ta bayyana rana

Jam'iyyar APC ta shirya taron NEC na gaggawa, ta bayyana rana

- Kakakin jam'iyyar APC, Yekini Nabena ya sanar da dage taron APC NEC

- Kamar yadda aka sanar a baya, za a yi taron ne a ranar 5 ga watan Disamba

- An mayar 8 ga watan Disamba a gidan gwamnati da ke Abuja da misalin 11 na safe

Kakakin jam'iyyar APC, Yekini Nabena, ya saki wata takarda da yammacin Lahadi, wacce ke nuna an dage taron da aka sanar za ayi na ranar 5 ga watan Disamba.

Dama daga fadar shugaban kasa za a tsara taron, jaridar Vanguard ta ruwaito hakan.

Kamar yadda takardar tazo; "An dage taron gaggawa wanda NEC ta jam'iyyar APC ta shirya zuwa ranar Talata, 8 ga watan Disamban 2020.

"Gayyatar da NEC ta jam'iyyar APC wacce sakataren tarayya na shugaban CECPC, Sanata John James Akpanudoedehe ya sanar a kan za a yi taron ya nuna an daga. Duba ga matsayin jam'iyya da kuma neman mataki na gaba da jam'iyya za ta dauka.

Jam'iyyar APC ta shirya taron NEC na gaggawa, ta bayyana rana
Jam'iyyar APC ta shirya taron NEC na gaggawa, ta bayyana rana. Hoto daga @Vanguardngrnews
Source: Twitter

KU KARANTA: Kalamai masu ratsa zuciya da Bashir Ahmad yayi ga matarsa ranar zagayowar haihuwarta

"Sakamakon bin dokar kare kai daga cutar COVID-19, an daga taron APC NEC. Za a yi taron da misalin karfe 11 na safe a ranar 8 ga watan Disamba a gidan gwamnati da ke Abuja".

A wani labari na daban, kungiyar gwamnonin arewa maso gabas sun bukaci gwamnatin tarayya ta bai wa jihohinsu damar yankewa duk wanda aka kama da laifin ta'addanci hukuncin da ya dace dashi.

Gwamnan jihar Borno, kuma shugaban kungiyar, Babagana Umara Zulum ne ya bukaci hakan a ranar Alhamis a wani taro da suka yi a Yola, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamna Zulum ya koka a kan yadda Antoni janar na tarayya ne kadai yake da damar yankewa 'yan ta'adda hukunci. Ya ce daukar 'yan ta'adda daga yankinsu har zuwa Abuja don yanke hukunci yana matukar bayar da wahala.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
APC
Online view pixel