Jawabi: Ministan gona ya taya ‘Yan Najeriya murnar shekara 60 da ‘yanci

Jawabi: Ministan gona ya taya ‘Yan Najeriya murnar shekara 60 da ‘yanci

- Muhammad Nanono ya bayyana cewa Najeriya ta fi kowa noma shinkafa

- Ministan ya ce Najeriya ta na da karfin da za ta iya ciyar Nahiyar Afrika

- Nanono ya yi jawabi domin taya ‘Yan Najeriya murnar samun ‘yancin kai

Ministan harkar gona da cigaban karkara, Muhammad Sabo Nanono ya yi jawabi domin taya ‘yan kasa murnar cika shekaru 60 da samun ‘yanci.

Alhaji Muhammad Sabo Nanono ya bayyana cewa akwai abubuwan da za su sa kasar ta yi murna da zuwan rana irin ta yau, 1 ga watan Oktoba.

Muhammad Sabo Nanono ya ke cewa duk da irin kalubalen da ake fuskanta a Najeriya, nasarorin da aka samu a Najeriya sun cancanci ayi murna.

KU KARANTA: Mutane sun ragargaji Buhari bayan ya yi jawabin Najeriya @ 60

Jawabi: Ministan gona ya taya ‘Yan Najeriya murnar shekara 60 da ‘yanci
Ministan gona, Sabo Nanono Hoto: FMARD
Asali: UGC

“Ina yi maku murna ‘yan Najeriya na cika shekaru 60 da samun ‘yanci a kasarmu. Murnar samun ‘yancin-kai abu ne da ya kamata ayi farin-ciki.”

Ministan harkar noman ya kara da cewa la’akari da nasarorin da aka samu duk da tulin kalubale.

“A shekarar 2019, Najeriya kasar da ta fi kowace noma a shinkafa a Nahiyar Afrika, ta doke kasar Masar a karon farko a tarihi.” Inji Sabo Nanono.

Mai girma Ministan ya kara da cewa: “Wadannan nasarorin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ne na babbako da sha’anin noma.”

KU KARANTA: Mutumin da ya fara kirkiro tutar Najeriya

“Mu na bukatar hadin-kai tsakanin gwamnati da manoma domin a inganta kokarinmu. Najeriya ta na da karfin da za ta ciyar da kasar nan da makwabta.”

Wannan jawabi na ministan ya fito ne a shafinsa na Tuwita, @NanonoSabo, a ranar Alhamis, 1 ga watan Oktoba, 2020.

Dazu kuma mu ka ji cewa wasu matasa sun shirya za su yi zanga-zangar juyin juya hali a ranar da ake bikin cika shekaru 60 da samun 'yanci a Osun.

A na cikin haka-haka ne dakarun DSS su ka tarwatsa masu zanga-zanga, su ka yi ram da su

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng