Shugaban kasa Buhari: Noma shi ne mafita ga matasa masu jini a jika

Shugaban kasa Buhari: Noma shi ne mafita ga matasa masu jini a jika

- Shugaba Buhari ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta farfado da fannin noma don samar da wadataccen abinci da kuma ayyukan yi

- A cewar shugaban kasar, mayar da hankali kan fannin noma zai rage dogaron kasar a kan danye mai

- A kan hakan, shugaban kasar ya shawarci matasa masu jini a jika, da su fantsama a fannin noma, domin kuwa noma ne mafita

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jaddada cewa gwamnatinsa ta dukufa wajen farfado da fannin noma don samar da wadataccen abinci da bunkasa tattalin arzikin kasa.

Shugaban kasar ya ce mayar da hankali a fannin noma zai taimaka wajen rashin dogaron kasar da fannin danyen mai, musamman wajen kasafin kudi.

Wasu daga cikin tsare tsaren shugaban kasar na farfado da tattalin arziki sun hada da rufe iyakokin kasa domin bunkasa noma shinkafa, da dakile masu shigo da abinci kasar.

KARANTA WANNAN: Tashin farashin man fetur da lantarki: Shawarar da Kwankwaso ya ba Buhari

Shugaban kasa Buhari: Noma shi ne mafita ga matasa masu jini a jika
Shugaban kasa Buhari: Noma shi ne mafita ga matasa masu jini a jika
Asali: Facebook

"Ina kara jaddada cewa daga yanzu babban bankin Nigeria ba zai kara bayar da canji ga masu shigo da abinci ko taki a kasar ba.

"Ba zamu biya ko kwabo na kudaden ajiyar waje ga masu shigo da kayan abinci ko taki ba. Maimakon hakan, zamu bunkasa manomanmu na cikin gida," cewar Buhari a ranar Alhamis.

Shugaban kasar ya kasance yana mai karfafa guiwar matasa akan su koma noma, kasancewar farashin danyen mai na ci gaba da durkushewar a kasuwar duniya.

Taken gwamnatin sa ya kasance, "Dole mu ci abunda muka noma, kuma dole mu noma abunda zamu ci."

Shugaban kasar ya dawo kan wannan take a makon da ya gabata. "Muna da matasa masu jini a jika da ke da burin aiki, to noma shi ne mafita ga kowa," a cewarsa.

KARANTA WANNAN: Janye tallafin man fetur: Gwamnatin tarayya ta fadi ayyukan da zata yi da kudaden

Shugaban kasar ya sha suka daga shekarar 2018 a lokacin da ya kira matasan kasar a matsayin "cima zaune".

Legit.ng Hausa ta ruwaito maku cewa a ranar 18 ga watan Afrelu 2018, a taron kungiyar kasashe masu takama da kasuwanci a Westminster, ya ce matasan Nigeria na jira gwamnati ta yi masu komai.

A wani labarin, Rabiu Kwankwaso ya bayyana cewa karin farashin man fetur da wutar lantarki a wannan lokacin zai kara jefa 'yan Nigeria cikin mawuyacin hali.

Ya bukaci shugaba Buhari da ya gaggauta janye karin, yana mai cewa kamata ya yi shugaban ya dinke barakar da ake samu a gwamnatinsa maimakon karin farashin man fetur da lantarki.

Kwankwaso wanda ya yi wannan kiran a zantawarsa da BBC Hausa ranar Juma'a ya ce babu wani kwakkwaran dalili na kara kudin fetur da lantarki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel