Bayan kisan Zabarmari, dakarun soji sun kaddamar da hari kan shugabannin Boko Haram a dajin Sambisa (bidiyo)

Bayan kisan Zabarmari, dakarun soji sun kaddamar da hari kan shugabannin Boko Haram a dajin Sambisa (bidiyo)

- Hedkwatar tsaro ta sanar da yan Najeriya labari mai dadi bayan kisan Zabarmari da yan ta’adda suka yi a Borno

- Bisa rahoton hedkwatar tsaron a ranar Talata, 1 ga watan Disamba, dakarun soji sun lalata mafakar shugabannin Boko Haram a dajin Sambisa

- Kakakinta, Manjo Janar John Enenche ne ya bayyana hakan a ranar Talata

Rundunar sojojin Najeriya ta dauki mataki kan yan ta’adda a Borno yan kwanaki bayan sun yi wa bayin Allah kisan kiyashi a jihar.

A cewar hedkwatar tsaro a ranar Talata, 1 ga watan Disamba, dakarun sojin Operation Lafiya Dole sun lalata mafakar shugabannin Boko Haram a dajin Sambisa.

A yayin aikinsu, rundunar sojin saman sun kuma kashe mayakan kungiyar da dama a Yale da ke jihar.

Bayan kisan Zabarmari, dakarun soji sun kaddamar da hari kan shugabannin Boko Haram a dajin Sambisa (bidiyo)
Bayan kisan Zabarmari, dakarun soji sun kaddamar da hari kan shugabannin Boko Haram a dajin Sambisa Hoto: @DefenceInfoNG
Source: Twitter

KU KARANTA KUMA: Yankin jihar Adamawa inda jama'a ke shan ruwa daya da dabbobinsu

Rundunar a cikin wata sanarwa daga jagoran labarai na ayyukan tsaron Manjo Janar John Enenche, ta ce:

“A ci gaban aikin da sojin sama ke aiwatarwa na Operation Wutar Tabki 2, dakarun sojin sama na Operation Lafiya Dole sun lalata wasu mafakar shugabannin kungiyar yan ta’addan Boko Haram sannan sun kashe mayakansu da dama a wasu hare-hare mabanbanta a dajin Sambisa da kuma gabashin Yale, duk a jihar Borno.

“An kai hare-haren saman ne a jiya, 30 ga watan Nuwamba 202, bayan samun bayanai na sirri sannan wasu bincike sun nuna cewa wasu yan Boko Haram da suka aiwatar da hare-haren bayan nan kan bayin Allah sun nemi mafaka a dajin Sambisa yayinda aka gano sauran a yankin gabashin Yale.”

KU KARANTA KUMA: Kayi murabus yanzu: Buhari na fuskantar matsin lamba yayinda dattawan arewa suka tunzura kan kisan Zabarmari

A gefe guda, Gwamnonin Arewa maso gabas sun goyi bayan kira ga gwamnatin tarayya a kan tayi amfani da sojojin haya wajen yaki da ta’addanci a yankin.

Gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku, ya bayyana hakan a ranar Talata, 1 ga watan Disamba, a madadin takwarorinsa a yayin wata ziyara da ya kai jihar Borno don yi wa gwamnati da mutanen jihar jaje.

Legit.ng ta tattaro a baya cewa mayakan Boko Haram sun kai wani mummunan hari kan manoma a garin Zabarmari wanda yayi sanadiyar rasa akalla rayuka 43.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel