NPF sun cusa sunayen Kurata 925 a jerin sababbin Jami’an ‘Yan Sanda inji PSC

NPF sun cusa sunayen Kurata 925 a jerin sababbin Jami’an ‘Yan Sanda inji PSC

- PSC ta ce an sa wadanda ba su nemi aikin ‘Yan Sanda ba cikin sababbin Kurata

- Hukumar kasar ta ce a karshe dole ta hakura da wannan aika-aika da NPF ta yi

- Mai magana da yawun PSC, ya ce mutane fiye da 900 ne aka cusa ta bayan fage

Hukumar da ke kula da harkar aikin ‘yan sanda a Najeriya, ta ce mutane 925 aka cusa ta bayan fage a cikin jerin sababbin kurata da za a dauka aiki.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa PSC ta na zargin Sufeta Janar na ‘Yan Sanda, Mohammed Adamu da yin wannan danyen aiki da ya saba wa doka.

A cewar PSC mutane 900 da aka ba aiki, ba su shiga cikin masu neman zama ‘yan sanda ba, sannan ba ayi masu gwaji ko wata irin tantance wa ba.

Hukumar ta bayyana wannan ne da take musanya zargin da ake yi mata na hana wasu jami’an ‘yan sanda da aka dauka aiki a shekarar bara kudinsu.

KU KARANTA: Ma’aikatan N-Power 1, 000, 000 za a dauka maimakon 500, 000

A ranar Talata, 1 ga watan Nuwamba, PSC ta fitar da jawabi ne ta bakin mai magana da yawunta, Ikechukwu Ani, ta ce babu ‘dan sandan da aka hana kudinsa.

Ani ya ce duk wadanda aka dauka aiki sun samu takarda, sannan an tantance su, an kuma yi masu rajista da IPPIS, ana jiran gwamnatin tarayya ta fara biyansu.

A cewar Ikechukwu Ani, an yi gyara game da wadanda aka dauka aikin ‘yan sanda bayan babban kotu ta ba hukumar nasara wajen shari’ar daukar aiki a kan NPF.

“Akwai bukatar mu kuma yi karin-haske cewa wajen daukar ‘yan sanda 10, 000, hukuma ta gano cewa an sa sunayen mutane 925 da ba su nemi wannan aiki ba.”

KU KARANTA: Lokaci ya yi da ya kamata a duba kwakwalwar Buhari – Ezekwesili

NPF sun cusa sunayen Kurata 925 a jerin sababbin Jami’an ‘Yan Sanda inji PSC
Shugaban ‘Yan Sanda Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

“Ba su bi matakan da ake bi na daukar aiki ba. Wannan sun hada da tantace wa, gwaji da jarrabawar lafiya.” Ani ya ce a karshe dole aka hakura aka dauke su.

Idan muka koma siyasar 2023, za mu ji cewa Gwamna Nasir El-Rufai ya fito ya bayyana cewa shi yana goyon bayan ‘Yan Kudu su karbi mulkin kasar nan a nan gaba.

Nasir El-Rufai ya ce ko da ba ya goyon bayan karba-karba, amma a 2023, a kai mulki Kudu, ganin cewa shugaba Muhammadu Buhari zai shafe shekaru takwas a kujera.

Gwamnan Kaduna yace shi a karon kansa, babu abin da ya dame shi da addini ko kabilar mutum.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel