Ina goyon-bayan mulkin Najeriya ya koma Kudu a 2023 inji Nasir El-Rufai
- Bayan Muhammadu Buhari, Nasir El-Rufai ya na ganin mulki zai koma Kudu
- Gwamnan Kaduna ya na bayan Fashola, ya nemi APC ta ba ‘Dan Kudu mulki
- Gwamna Nasir El-Rufai yace a karon kansa, ba ya goyon bayan karba-karba
Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi kira ga jam’iyyarsu ta APC mai mulki, ta cika abu mai kama da alkawarin da ta yi game da zaben 2023.
Malam Nasir El-Rufai yana so jam’iyyar APC ta tabbata mulkin Najeriya ya koma hannun ‘dan Kudu.
Gwamnan na APC ya bayyana haka ne a lokacin da aka yi hira da shi a shirin siyasa na Politics Today a gidan talabijin na Channels TV a ranar Litinin.
Jaridar The PUNCH ta bi wannan hira da aka yi da gwamnan Kaduna, inda aka tabo masa maganar da ake yi game da Magajin Muhammadu Buhari.
KU KARANTA: APC ta mutunta tsarin karba-karba - Fashola
El-Rufai yake cewa: “Ya kamata in yi wannan karin-haske. Ni a karon kai na, bana goyon bayan tsarin karba-karba.”
Gwamnan ya cigaba da bayani: “Domin babu kasar da ta cigaba ta hanyar la’akari da inda shugabanninta suka fito, addininsu, ko kabilarsu.”
“Ba na goyon bayan wannan, kuma ba na aiki da shi. Ina aiki da mutane daga duk inda su ka fito a fadin kasar nan. Babu abin da ya dame ni da addinsu ko kabilarsu.”
El-Rufai ya ce abin da ke gabansa kawai shi ne ya ga an yi aiki, amma ya ce wannan ra’ayin kansa ne. Kuma har yanzu APC ba ta fitar da matsaya a kan wannan ba.
KU KARANTA: Sai Buhari ya zarce Yarbawa za su samu mulki
Amma duk da haka, Gwamna El-Rufai ya na ganin bayan Buhari ya kammala wa’adinsa, ya kamata mulki ya koma hannun kowane bangare a yankin Kudu.
Kwanakin baya kun ji cewa Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, ya ce APC za ta cigaba da mulki a 2023, matsawar sun cika alkawuran da su kayi a baya.
Ministan ya ce wajibi ne 'yan siyasa su dage wurin cika alkawuran da suka daukar wa al'umma don hakan ne abinda ya kamata idan suna so su cigaba da mulki.
A cewar tsohon gwamnan, mutanen Najeriya za su zabi jam'iyyar da ta cika alkawuranta ne.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng