Fayose ya ce FG za ta hukunta yan majalisar da suka aika sammaci ga Buhari kan rashin tsaro

Fayose ya ce FG za ta hukunta yan majalisar da suka aika sammaci ga Buhari kan rashin tsaro

- Ayodele Fayose, tsohon gwamnan Ekiti ya yi zargin cewa FG za ta dauki matakai masu tsauri kan yan majalisar wakilai da suka nemi a gayyaci Buhari zaurensu

- Fayose ya ce kwanan nan za a ji hukumar EFCC na gayyatar yan majalisar tare da daskarar da asusun bankunansu

- A ranar Talata ne dai majalisar ta aika sammaci ga Shugaban kasar kan matsalar tsaro a kasar bayan kisan Zabarmari

Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose, ya fada ma yan majalisar wakilai da su shirya fuskantar hukunci masu tsauri daga gwamnatin Najeriya kan sammaci da suka aika wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari don ya gurfana a gaban majalisar.

Fayose ya yi jawabin ne a ranar Talata, 1 ga watan Disamba, yayinda yake martani a kan sammacin da yan majalisar suka aikawa Shugaban kasar domin ya sanar da majalisa gaskiyar lamari kan halin da tsaron kasar ke ciki.

KU KARANTA KUMA: Kayi murabus yanzu: Buhari na fuskantar matsin lamba yayinda dattawan arewa suka tunzura kan kisan Zabarmari

Fayose ya ce FG za ta hukunta yan majalisar da suka aika sammaci ga Buhari kan rashintsaro
Fayose ya ce FG za ta hukunta yan majalisar da suka aika sammaci ga Buhari kan rashin tsaro Hoto: Muhammadu Buhari, Ayo Fayose, House of Reps
Asali: Facebook

Tsohon gwamnan ya yi zargi a shafin Twitter cewa gwamnati za ta fara tozarta yan majalisar da suka jagoranci kira ga gayyatar ta wadannan hanyoyin:

1. Ya bayyana cewa yan majalisar su tsammaci samun gayyata daga hukumar yaki da cin hanci da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC).

2. Fayose ya yi ikirarin cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa za ta daskarar da asusun yan majalisar na wakilai.

3. Tsohon gwamnan ya kuma yi zargin cewa ana iya kama yan majalisar kan zargin yunkurin kai gwamnatin Buhari kasa.

Sai dai kuma, dan majalisar ya bayyana cewa zai yi mamaki idan har Shugaban kasar ya yanke shawarar amsa gayyatar.

KU KARANTA KUMA: Gaskiyar dalilin da yasa har yanzu Buhari ke ajiye shugabannin tsaro, Garba Shehu

Fayose ya kuma ci gaba da caccakar yan majalisa masu ci a majalisar dokokin tarayya. Ya ce yan majalisar wadanda ya kamata su wakilci mutane sun zama kamar karnuka marasa hakora.

A baya mun ji cewa, majalisar wakilai ta aika sammaci ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari akan kisan manoma 43 a garin Zabarmari da ke jihar Borno.

Yan majalisar sun yanke shawarar ne a ranar Talata yayinda suka aminta da wani jan hankali da Satomi Ahmed yayi na cewa hakan na da matukar muhimmanci.

Da fari mun ji cewa hatsaniya ya kaure a majalisar wakilai kan wani kudiri da aka gabatar na neman a gayyato Buhari don ya amsa tambayoyi a kan hauhawan rashin tsaro a kasar.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel