Matashin da ke samun 20,000 a wata ya siya wa budurwarsa abincin 4,500
- Wani saurayi dan Najeriya ya bayyana irin wahalar da ya sha a soyayyarsa da wata budurwa
- Ya ce budurwar ta bukaci cin abincin N4500 daga sun fita yawo,kuma lokacin albashinsa N20,000 ne
- Ya yi wallafar ne a shafinsa na Twitter, inda ya sha caccaka har wasu suke ganin budurwar bata da laifi
Wani dan Najeriya mai suna Olusegun ya bayyana irin bakar wahalar da ya fuskanta a soyayya lokacin yana daukar albashin N20,000.
Saurayin ya wallafa labarin abinda ya faru tsakanin shi da budurwarsa a kafar sada zumuntar zamani ta Twitter.
A cewarsa, sun dan fita yawon shakatawa da shi da budurwarsa, ya siya wa kansa ruwa, ita kuma budurwar ta bukaci abincin N4500.
KU KARANTA: Gazawar shugaban kasa wurin bada tsaro abu ne da zai sa tsigesa, Osinbajo a 2015
Olusegun ya ce tun daga ranar ya fahimci cewa budurwar ba matar da ya dace ya karasa rayuwarsa da ita bace.
Matsayin mace da namiji ba daya bane, ya kamata mace ta dinga tausayin mijinta. Tun bayan ganin wannan wallafar, wata budurwa 'yar Najeriya ta ce bai kamata a ce namiji yayi soyayya ba, idan ya san ba shi da isasshen kudi.
Wannan wallafar tasa ta janyo cece-kuce a kafar sada zumuntar zamanin, inda wani DayoOluyede yace: "Gaskiya kana da matsala, kada ka cigaba da irin wannan tunanin. Bata dace da zama matar aure ba? Saboda ta bukaci abinci yayin da ka bukaci ruwa? Ka fadi mata iyakar kudin da kake da su ne? Ta san nawa ne albashinka? Ko kuma ita ta kai kanta wurin cin abincin?"
KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan bindiga sun halaka manoma 7, sun sace mutum 30 a Katsina
Wani t_enabler cewa yayi: "20,000 duk wata kake dauka? Amma baka yi wani tunani ba sai ka fitar da budurwa zuwa wurin shakatawa? Ba ka yi tunanin fara kulawa da kanka ba, har ka fara tunanin ciyar da mutane 2?"
Wani LufadejuD ya yi tsokaci da: "Fitar da budurwa shakatawa baya nufin cin abinci za ku je yi. Kawai 'yan matan yanzu mayun abinci ne."
A wani labari na daban, wani mugun fada da aka yi a kan soyayyar budurwa ta sa an kashe mutum daya a Jalingo, babban birnin jihar Taraba.
Gidan talabijin na Channels ya ruwaito yadda aka yi fadan a yankin gidan ruwa na Jalingo wanda ya janyo asarar kadarorin miliyoyin naira.
An gano cewa fadan ya koma na addini saboda daya daga cikin samarin ya yi hayar 'yan daba domin tada hankula. Dayan saurayin kuwa ya kira abokansa ne domin su taimaka masa samun nasara.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng