Boye matar aure: Wata kotu a Kano ta bukaci Rarara da ya bayyana a gabanta
- Babbar kotun shari'a da ke Kano ta bukaci Dauda Kahutu Rarara ya bayyana a gabanta kafin ranar 22 ga watan Disamba
- Hakan ya biyo bayan korafin da mijin wata mata ya kai gaban kotu bayan Rarara ya tsere masa da matarsa
- A cewar mijin, watanni 3 kenan da ya nemi matarsa ya rasa tun bayan ta bayyana a wani bidiyon wakar Rarara
Babbar kotun shari'a ta Kofar Kudu da ke jihar Kano ta gayyaci babban mawakin Shugaba Muhammadu Buhari, Dauda Kahutu Rarara, inda ta bukaci ya gabatar da kansa gaban kotu kafin ranar 22 ga watan Disamba a kan zargin boye wata matar aure, wacce yayi wani bidiyon wakarsa.
Bayan mijin matar ya gabatar da korafinsa a gaban kotun, inda ya zargi mawakin da amfani da matarsa, matar aure a bidiyon wata wakarsa mai taken 'Jihata', wanda tun bayan nan bai sake ganinta ba.
Ya kai korafin gaban kotu bayan ya yi watanni 3 cur, ba tare da ya san inda matarsa take ba, kuma ya bukaci kotun da tayi masa adalci a kan wannan wulakanci da aka yi masa, Daily Trust ta tabbatar.
KU KARANTA: 'Yan sandan da ya dace su yaki 'yan bindiga ne ke rike jakar matan manya, El-Rufai
KU KARANTA: Kisan Zabarmari: Duk malamin da bai yi huduba a kan tsaro ba munafuki ne, Malam Maraya
Alkalin kotun musuluncin, Ustaz Ibrahim Sarki Yola, ya dage sauraron shari'ar zuwa 22 ga watan Disamba don Rarara ya bayyana a gaban kotu, a cigaba da sauraron shari'ar.
A wani labari na daban, Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayyana damuwarsa a kan rashin damar bayar da umarni ga 'yan sanda a kan kashe-kashe da tabarbarewar tsaro a Najeriya.
A wata tattaunawa da gidan talabijin din Channels suka yi da gwamnan a ranar Litinin, 30 ga watan Nuwamba, El-Rufai ya bayyana damuwar da shi da takwarorinsa na sauran jihohi suka shiga a kan harkokin tsaron kasar nan.
Gwamnan ya ce ana kiran gwamnoni da shugabannin jami'an tsaro ne a baki kawai, amma a zahiri, basu da damar tankwara 'yan sanda.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng