Karyewar darajar Naira akan Dala: Ƴan Nigeria sun yi cece-kuce

Karyewar darajar Naira akan Dala: Ƴan Nigeria sun yi cece-kuce

- Yayinda tattalin arzikin Najeriya ya shiga yanayi na matsi, darajar na kara karyewa a kasuwar canji

- A yanzu ana siyar da dalar Amurka daya kan naira 500 a kasuwar hada-hada

- Yan Najeriya sun tofa albarkacin bakunansu, da dama sun nuna rashin jin dadinsu kan haka

Matsalar karyewar tattalin arziki na neman zame wa ‘yan Najeriya gaba damisa baya siyaki, inda aka wayi gari darajar dalar Amurka daya ta kai daidai da naira 500 a kasuwar canji.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da gwwamnatin tarayya ta bayyana cewa halin matsin tattalin arzikin kasar ke ciki ba zai dauki dogon lokaci ba.

Ministar kudi da tsare-tsare ta kasa, Misis Zainab Ahmed ce ta bayyana hakan a ranar Litinin, 23 ga watan Nuwamba, a taron tattalin arziki karo na 26 wanda aka fara a babbar birnin tarayya, Abuja.

Karyewar darajar Naira akan Dala: Ƴan Nigeria sun yi cece-kuce
Karyewar darajar Naira akan Dala: Ƴan Nigeria sun yi cece-kuce Hoto: @PremiumTimesng
Source: Twitter

Sai dai kuma duk da hakan darajar Naira na kara karyewa yayinda na dalar Amurka ke tashin gwauron zabi a kasuwar bayan fage.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Hatsaniya ya kaure a majalisa kan bukatar gayyatar Buhari

Hakan ya sanya yan Najeriya da dama a shafin soshiyal midiya nuna damuwarsu da alhinin halin da kasar ke ciki.

Ga sharhin wasu daga cikinsu a shafin Legit.ng Hausa na Facebook:

Wani mai amfani da shafin Facebook mai suna Unique Abdoul ya bayyana cewa kasar ma gaba dayanta faduwa take yi ba naira kadai ba.

Ya ce: “Kasar ma gaba daya faduwa takeyi ba iya naira ba. Allah ya isar mamu.”

Abba Labaran ya ce: “Ya Allah Kaine mai canza dukkan kunci zuwa walwala, ya Allah Kaine mai ikon akan kome Kaine shugaban da Babu kamarsa kome a wurinka yake kuma kome sai kaga dama yake faruwa Allah ka kawomana sauki a kasarmu Nigeria dama sauran kashen musulmi.”

Aliyu Nuhu Kt ya ce: “Haqiqa yanzu mudamuki qasashin wajemunemukasan chinjin naira yalalachi saikajezaka turama da stuhi kudi ko yan uwa saikaga abunkullum chibaya akeye Shiyasama niwani lokachinbani ganin stadar abunchi A Nigeria domunkuwa kudinqasarne gabadaya sunlalachi. Ammamu yanzu bashineyadame muba Abunda yadamemu shine mastalar staro. Saikashemu akeye amma anqidaukarmataki allah kakawoma. Yan uwanmu Arewa dauki.”

Abubakar Muhammad Maigana ya ce: “To miye gamin talaka da dala. Chan tamatse musu suje su karata da ita.”

KU KARANTA KUMA: Gaskiyar dalilin da yasa har yanzu Buhari ke ajiye shugabannin tsaro, Garba Shehu

Mujahid Muhammad ya ce: “Buhari dai ya sheke mutuncin naira.”

Abdullahi Al-katsinawy Muhammad ya ce: “Qasar Nan ma sauka takeyi ballantana wata Dollar.”

A wani labarin, Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da rokon gwamna Abdullahi Umar Ganduje na nemo aron kudi daga babban bankin Najeriya watau CBN.

Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar 1 ga watan Disamba, 2020, cewa gwamnatin Kano za ta karbo wannan kudi ne ta hannun wani bankin kasuwa.

A zaman da majalisar dokokin ta yi a ranar Litinin, kakakin majalisa, Rt. Hon. Abdulazeez Garba-Gafasa, ya karanto takardar da gwamnan ya aiko.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel