FG ta bayyana lokacin da Najeriya za ta fita daga karayar tattalin arziki

FG ta bayyana lokacin da Najeriya za ta fita daga karayar tattalin arziki

- Ministar kudi ta kasa, Zainab Ahmed ta bayyana cewa matsin tattalin arziki da Najeriya ta shiga na dan lokaci ne

- Zainab ta sanar da hakan ne a taron tattalin arziki da ke gudana a Abuja a yau Litinin, 23 ga watan Nuwamba

- A ranar Asabar ne alkallumar kiddigar abinda kasa ke samu suka nuna cewa Najeriya ta sake shiga matsin tatallin arziki a hukumance

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa karayar tattalin arziki da Najeriya ta fada ciki a yanzu ba zai dauki dogon lokaci ba.

Ministar kudi da tsare-tsare ta kasa, Misis Zainab Ahmed ce ta bayyana hakan a ranar Litinin, 23 ga watan Nuwamba, a taron tattalin arziki karo na 26 wanda aka fara a babbar birnin tarayya, Abuja.

Ta ce: “Karayar tattalin arziki da aka fada ciki zai kasance na dan kankanin lokaci ne kuma masu ruwa da tsaki sun fara aiki tare domin samar da matakan da za su magance tare da inganta lamarin.”

FG ta bayyana lokacin da Najeriya za ta fita daga karayar tattalin arziki
FG ta bayyana lokacin da Najeriya za ta fita daga karayar tattalin arziki Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

Hukumar kididdiga ta kasa ta sanar da cewar Najeriya ta sake fadawa a matsalin tattalin arziki a ranar Asabar, 21 ga watan Nuwamba.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Tsohuwar kwamishinar lafiya ta jihar Bauchi Zuwaira Hassan ta rasu a hatsarin mota

Taron Tattalin Arzikin Kasa karo na 26, an shirya shi ne da hadin guiwar Ma’aikatar kudi, kasafi da tsarin kasa (FMFBNP), jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Taron zai ba masu ruwa da tsaki a gwamnati da kamfanoni damar yin nazari tare da kawo mafita ga halin da aka tsinci kai, musamman yadda annobar COVID-19 ta yi tasiri ga tattalin arzikin Najeriya.

A baya mun ji cewa a hukumance, Najeriya ta fada cikin halin matsin tattalin arziki mafi muni cikin shekaru fiye da 30.

A cewar rahoton kiddidigar abinda kasar ke samarwa a shekara, GDP, ta Hukumar Kididdiga na Kasa, NBS, ta fitar a ranar Asabar, hada-hadar kasuwanci sun ragu da kashi 3.62 cikin 100 a watanni uku na karshen 2020.

KU KARANTA KUMA: An damke madugun mai garkuwa da mutane da mai yi wa yan bindiga leken asiri a Katsina da Zamfara

Wannan shine karo na biyu da GDP din ke raguwa a jere tun matsin tattalin arzikin da kasar ta fada a shekarar 2016.

Jumullan GDP din na watanni tara na farkon shekarar 2020 sun nuna alkallumar na -2.48%.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel