Gwamna Zulum ya jagoranci jana’izar manoma 43 da Boko Haram ta yi wa yankan rago a Borno

Gwamna Zulum ya jagoranci jana’izar manoma 43 da Boko Haram ta yi wa yankan rago a Borno

- Gwamna Zulum ya jagoranci jana'izar manoma 43 da Boko Haram ta yi wa yankan rago a Zabarmari da ke jihar Borno

- An tattaro cewa har yanzu ba a gama tantance adadin wadanda aka kashe ba da kuma wadanda suka bata

- A daren ranar Asabar ne dai maharan suka abka wa manoman yayin da suke girbin shinkafa kauyen Koshebe da ke karamar hukumar Mafa

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya jagoranci jana’izar mutane 43 da mayakan Boko Haram suka yi wa yankan rago a yankin Zabarmari ta jihar.

Koda dai wadanda aka kashen suna zama ne a Zabarmari, wani garin manoman shinkafa da ke karamar hukumar Jere, an kai masu hari ne a ranar Asabar, a kauyen Koshebe, a karamar hukumar Mafa.

A safiyar yau Lahadi, 29 ga watan Nuwamba, ne Zulum ya yi wa garin tsinke inda mazauna yankin suka sanar masa da cewa har yanzu ba a gama tantance yawan mutanen da aka halaka ba da kuma wadanda suka bata.

Gwamna Zulum ya jagoranci jana’izar manoma 43 da Boko Haram ta yi wa yankan rago a Borno
Gwamna Zulum ya jagoranci jana’izar manoma 43 da Boko Haram ta yi wa yankan rago a Borno Hoto: @GovBorn
Asali: Twitter

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar a shafinta na Facebook.

KU KARANTA KUMA: An yi nadin manyan muhimman sarautu guda 7 a masarautar Katsina

“Ya mai girma, kamar yadda ka gani a nan, gawawwaki 43 aka binne, amma ba a samo wasu daga wajen da lamarin ya afku ba. Babu wanda zai iya cewa ga ainahin yawan mutanen da aka kashe. Har yanzu ba a ga wasu daga cikin mutanen ba,” wani mazaunin yankin ya sanar da gwamnan.

Gwamna Zulum ya yi jaje ga al’umman garin yana mai cewa: “Da farko, ina mai mika jajena a kan wannan barnar, wacce ta shafi dukkaninmu da duk wani mutum ai imani. An sanar dani cewa har yanzu ba a ga wasu ba. Muna ta tattaunawa da sojoji tun jiya, Insha Allah za a gano sauran ba tare da bata lokaci ba.

"Abun damuwa ne cewa an yanka mutane fiye da 40 yayinda suke aiki a gonakinsu. Mutanenmu na cikin wani yanayi, suna a tsaka mai wuya, a bangare guda idan suka zauna a gida yunwa na iya kashe su, a bangare guda kuma, idan suka fita gonakinsu suna iya fuskantar barazanar kisa daga yan ta’adda. Wannan abun bakin ciki ne.

“Har yanzu muna rokon gwamnatin tarayya a kan ta dibi karin matasanmu da ke CJTF da maharbaa aiki a rundunar sojjin kasa domin su ba manoma kariya. Muna bukatar tsaro da yawa domin kare gonaki kuma matasanmu sun fahimci shimfidar wurin sosai. Ba za mu yanke kauna ba saboda har yanzu muna da yakinin kawo karshen ta’addanci,” in ji Zulum.

KU KARANTA KUMA: An gano Ndume tare da Jonathan yan kwanaki bayan sakinsa daga kurkukun Kuje

A baya mun kawo cewa yan Boko Haram sun kashe manoman shinkafa a kalla guda 44 a yayin da suke gurbe amfanin gonarsu a cewar dan majalisa da wasu majiyoyi.

Majiyoyi daga Zabarmari, wani gari a Borno da ya yi fice wurin noman shinkafa sun sanar da Premium Times cewa an kai wa manoman hari ne a lokacin da suke aiki a gonakinsu da ke Garin Kwashebe.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng