‘Yan bindiga sun hallaka Malamin Jami’ar Tarayya a Makurdi, Benuwai
-Jami’an tsaro sun tsinci gawar wani Malami a Jami’ar aikin gona, Makurdi
-An iske Dr. Karl Kwaghger jina-jina a hanya bayan an yanka makwogoronsa
-Zuwa yanzu babu wanda ya san wadanda su ka yi wannan danyen aiki a jihar
Rahotanni su na bayyana mana cewa ‘yan bindiga sun hallaka wani malamin makaranta a jami’ar koyon harkar noma a Makurdi, jihar Benuwai.
Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto cewa wannan lamarin ya auku ne a yankin gidauniyar J.S Tarka a cikin unguwar Makurdi da ke jihar Benuwai.
Daga baya an fahimci cewa Dr. Karl Kwaghger ne malamin da ya mutu a hannun wadannan miyagu.
KU KARANTA: NEGF: Zulum da sauran Gwamnoni sun koka da rashin tsaro
Karl Kwaghger ya kai matsayin mataimakin farfesa a sashen fasaha a jami’ar tarayyar ta FUAM. Da nan da 'dan lokaci kadan zai kure harkar boko.
Jaridar ta ce sai da wadannan mutane su ka fara rotsa kan Karl Kwaghger da wani abu mai matukar karfi, sannan sai aka yanka masa makwogoro.
‘Yan bindigan sun yi maza-maza sun tsere bayan sun yi wannan aika-aika, kuma rahotanni sun nuna har yanzu ba a gano wadannan mahara ba.
KU KARANTA: CNG ta yi kaca-kaca da Shugabanni kan matsalar tsaro
Shugaban kungiyar ASUU na reshen jami’ar FUAM, Dr. Ameh Ejembi, ya tabbatar wa manema labarai da mutuwar wannan abokin aikin nasa dazu.
Ita ma shugabar hulda da jama’a ta FUAM, Rosemary Waku ta fadawa Punch, babu shakka sun rasa ma’aikacinsu, amma ba ta bayyana yadda ya mutu ba
‘Yan sanda sun dauki gawar mutumin sun adana a dakin ajiya. Za a binciki abin da ya kashe sa.” Inji Kakakin ‘yan sandan Benuwai, Catherine Anene.
Kun ji cewa an gano ainihin yawan Bayin Allah da aka kashe a harin Zabarmari. Alkaluma sun nuna ainihin adadin mutanen da aka kashe ya zarce 40.
Wadanda aka yi wa yankan rago a harin Boko Haram na ranar Asabar sun haura mutum 110
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng